Ta fasu: an bayyana makudan biliyoyin da wani Gwamna ya kashe wajen yawo a jirgi

Ta fasu: an bayyana makudan biliyoyin da wani Gwamna ya kashe wajen yawo a jirgi

Ma’aikatan jihar Ekiti a karkashin inuwar ‘Wayayyun ma’aikatan jahar Ekiti (EWF) tare da hadin gwiwar kungiyar masu mutunci na Ado Ekiti AIG, sun zargi gwamnan jahar, Ayodele Fayose da kashe zambar kudi naira biliyan uku wajen yawo a jirgin sama.

Ma’aikatan sun bayyana kashe wadannan makudan kudade a matsayin almubazzaranci, wanda bai kawo ma al’ummar jahar Ekiti cigaba bat un bayan hawan Fayose kujerar gwamnan jahar a shekaru hudu da suka gabata.

KU KARANTA: Addu'ar lashe zabe: Wasu 'yan Kwankwasiyya sun gudanar da Sallah, saukar al'qur'ani da yanka

Jaridar daily trust ta ruwaito ma’aikatan a cikin sanarwar da suka fitar suna kira da a tuhumi gwamnan sakamakon yin sama da fadi da kudaden al’ummar jahar Ekiti ya zuba a harkokinsa na kasuwanci, kamar yadda shugaban hadakan, Mike Bamidele ya sanar.

Ta fasu: an bayyana makudan biliyoyin da wani Gwamna ya kashe wajen yawo a jirgi

Fayose
Source: Depositphotos

“Muna da kwararan hujjoji dake nuna yadda gwamna Fayose yake kashe makudan kudade wajen daukan hayan jirage da suke shawagi dashi wajen yawace yawacen hutawa tare da iyalansa da abokansa a ciki da wajen kasar nan.

“A cikin watan 47 daya kwashe yana gwamna, Fayose yayai tafiye tafiye da basu da iyaka, kuma binciken da muka yi a ma’aikatan sufurin jirage ya nuna gwamnan na kashe naira miliyan 26 a duk wata wajen yawace yawace.

“Binciken ya nuna ana biyan dala 2,500 a kowani awa daya da aka yi a jirgin yawo, sa’annan tafiyar jeka ka dawo na cin dala dubu ashiri zuwa dala dubu arba’in, a haka ma ya danganta da wanda ya hayi jirgin, saboda wasu ka iya shanya jirgin har sai yadda hali yayi.” Inji kungiyar.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito ma’aikatan na cizan yatsa na rashin tabuka komai a lokacin da wani hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ja musu kunne game da yawace yawacen da gwamnan yake yi da kudin gwamnatin.

Shima wani jigo a kungiyar, Dakta Sikiru ya bayyana yadda Fayose ya hana Sarakan gargajiyar jahar albashi, da kuma yadda ma’aikata suka rasa albashi na tsawon watanni tare da halin da yan fansho suka shiga a zamanin Fayose wanda yayi sanadin mutuwar mutane da dama.

Sai dai Gwamna Fayose ya musanta dukkanin zarge zargen nan, inda ya bayyana kungiyoyin a matsayin munafukai wadanda basu da tudu balle madafa, sa’annan yace wasu ne suka dauki nauyinsu.

“Ina kira ga munafukan dake daukar nauyin wasu mutane da sunan ma’aikatan jahar Ekiti akan wai gwamna ya dauki hayar jirgi yayi yawo da cewa idan sun rasa jirgin yan kasuwa a filin sauka da tashin jirage na Akure, su kama hanyar Abuja a akan dan achaba ko kuma akan jaki.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel