Gwamna Fayose ya fara banbami bayan Hukumar EFCC ta fara dakun sa

Gwamna Fayose ya fara banbami bayan Hukumar EFCC ta fara dakun sa

Mun samu labari cewa Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta aikawa Shugaban Hukumar Kwastam takarda cewa ka da ta bari Ayodele Fayose ya fice daga kasar nan.

Hukumar EFCC ta fara dakun Gwamnan Jihar Ekiti Ayo Fayose

Fayose yana cikin wadanda EFCC za ta taso keyar su
Source: Depositphotos

EFCC tana zargin Gwamnan na Ekiti da wa'adin sa ya kusa karewa da laifin satar dukiyar Gwamnati da kuma barna da cin amanar Kasa. Yanzu dai EFCC ba za ta iya taba Fayose ba har sai ya sauka daga mulki don haka ta ke jira zuwa watan gobe.

Gwamnan na PDP yayi watsi da binciken da EFCC ke shirin yi inda yace bai ki gobe ya fuskanci Hukumar ba. Fayose yace siyasa a binciken da ake neman yi masa amma duk da haka ba ya tsoron komai domin mutane ne su ba Ubangiji ba.

KU KARANTA: An kama wani 'Dan siyasa yana wanka da jini a Najeriya

Ayo Fayose ya fadawa EFCC su saurare sa Ranar 16 ga Watan Oktoba lokacin da wa'adin sa zai kare. Gwannan dai ya nuna cewa akwai sakarci a lamarin Hukumar ta EFCC mai yaki da barayi da ta jefa sunan sa cikin 'yan siyasan da za a kama.

Kwanan nan Gwamnan ya soki Shugaba Buhari kamar yadda ya saba inda ya nuna cewa Shugaban kasar mutum ne maras hakuri da kuma rashin iya rike adawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel