Yadda aka fara daura Jonathan kan kujerar mulkin Najeriya - Inji Tambuwal

Yadda aka fara daura Jonathan kan kujerar mulkin Najeriya - Inji Tambuwal

Labari ya zo mana daga The Cable na yadda Tsohon Shugaban Majalisar Wakilan Tarayya Aminu Tambuwal ya bada labarin yadda Goodluck Jonathan ya dare kan mulkin Kasar nan a 2010.

Yadda aka fara daura Jonathan kan kujerar mulkin Najeriya - Inji Tambuwal

Tsohon Shugaban kasa Jonathan da Sanata Mark da Tambuwal
Source: Depositphotos

Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana wannan ne lokacin da ya ziyarci Gwamnan Jihar Bayelsa Seriake Dickson domin yi masa ta'aziyya na rashin Mahaifiyar sa da yayi. A nan ne Gwamnan ya bada labarin abin da ya faru a baya.

Gwamnan na Jihar Sokoto yace irin su Seriake Dickson su ka same sa lokacin yana cikin manyan Majalisa inda su ka nemi a tabbatar da Jonathan ya gaji Marigayi Ummaru Yaradua domin ganin cewa kasar Najeriya ta zauna lafiya.

KU KARANTA: Buhari ya karbi bakuncin babban Shehi Dahiru Bauchi a fadar sa

Hakan dai kuma aka yi Jonathan ya hau mulki bayan Yaradua ya bar Duniya. Tambuwal yace su ne su ka shirya yadda aka yi Jonathan ya tabbata a matsayin Shugaban kasa a tsakiyar 2010. Tambuwal yace ba tun yau ya san Dickson ba.

Wannan abubuwan sun faru ne tun lokacin shi Gwanna Seriake Dickson yana Kwamishinan shari'a a Bayelsa. Dickson ya godewa Tambuwal da ta'aziyyar da yayi masa inda yace irin su Tambuwal sun dade su na aikin ganin Najeriya ta zauna lafiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel