Kuma dai: Daya daga cikin sanatocin APC da suka koma PDP ya fice daga jam’iyyar

Kuma dai: Daya daga cikin sanatocin APC da suka koma PDP ya fice daga jam’iyyar

Tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Barnabas Gemade, ya sanar da canjin shekarsa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar SDP.

Gemade na daya daga cikin sanatocin jam’iyyar APC da a kwanakin baya suka canja sheka zuwa PDP.

Da yake bayar da dalilin ficewarsa daga PDP, Gemade, ya bayyana cewar ya fita ne sabod cin amnarsa da gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom, ya yi a kan batun tikitin takarar sanatan gabashin jihar Benuwe.

Kuma dai: Daya daga cikin sanatocin APC da suka koma PDP ya fice daga jam’iyyar

Barnabas Gemade
Source: Depositphotos

A wani labarin na Legit.ng mai alaka da wannan, kun ji cewar a ranar 27 ga watan Agusta ne tsohon shugaban jam'iyyar PDP a jihar Legas, Mista Moshood Salvador, ya bayyana cewar ya koma jam'iyyar APC, kuma a jiya Asabar ne aka yi bikin karbar sa a Legas.

DUBA WANNAN: Daga karshe: IBB ya zabi wanda goyawa baya daga cikin 'yan takarar PDP

Yanzu haka Salvador tare da wasu manyan 'ya'yan jam'iyyar PDP sun shiga cikin sahun masu fada a ji a jam'iyyar APC a jihar Legas.

Da yake magana da wakilin kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) jiya a Legas, Salvador ya ce ya fita daga PDP ne bayan dukkan kokarinsa na dora jam'iyyar a kan hanya ta gari ya ki yiwuwa saboda son rai na wasu dattijan jam'iyyar a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel