Tsohon shugaban PDP ya fita daga jam'iyyar, ya fadi dalili

Tsohon shugaban PDP ya fita daga jam'iyyar, ya fadi dalili

A ranar 27 ga watan Agusta ne tsohon shugaban jam'iyyar PDP a jihar Legas, Mista Moshood Salvador, ya bayyana cewar ya koma jam'iyyar APC, kuma a jiya Asabar ne aka yi bikin karbar sa a Legas.

Yanzu haka Salvador tare da wasu manyan 'ya'yan jam'iyyar PDP sun shiga cikin sahun masu fada a ji a jam'iyyar APC a jihar Legas.

Da yake magana da wakilin kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) jiya a Legas, Salvador ya ce ya fita daga PDP ne bayan dukkan kokarinsa na dora jam'iyyar a kan hanya ta gari ya ki yiwuwa saboda son rai na wasu dattijan jam'iyyar a jihar.

Tsohon shugaban PDP ya fita daga jam'iyyar, ya fadi dalili

Moshood Salvador
Source: UGC

Kazalika Salvador ya karyata zargin cewar Tinubu ya saye shi zuwa APC domin a durkusar da jam'iyyar PDP a jihar Legas.

Salvador ya ce fitar sa daga PDP ta tabbatar da cewar yanzu jam'iyyar ta mutu murus a jihar Legas.

DUBA WANNAN: Babachir da Ribadu sun hada kai domin yakar sakataren gwamnatin Buhari

Tsohon shugaban jam'iyyar ya yi godiya ga jagoran APC na kasa, Bola Tinubu, mutumin da ya ce dama can abokinsa tun suna tsohuwar jam'iyyar AD tare.

Kazalika ya yi alkawarin bayar da muhimmiyar gudunmawa domin ganin jam'iyyar APC tayi nasarar a kowanne mataki a zabukan 2019.

Salvador ya dade yana fama da matsaninciyar adawa daga tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na kasa kuma dan asalin jihar Legas, Cif Bode George.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel