Haihuwar uwar sa: Matasa sun kama wani fitaccen dan siyasa yana wanka da jini tsirara

Haihuwar uwar sa: Matasa sun kama wani fitaccen dan siyasa yana wanka da jini tsirara

- An kama wani fitaccen dan siyasa a Najeriya yana wanka tsirara

- Matasan sun ce da jini suka kamashi yana wankan

- Sunan shi Honorabul Timothy Owoeye daga jihar Osun

Wasu matasa a jihar Osun dake a shiyyar kudu maso yammacin Najeriya sun cafke wani fitaccen dan siyasa a jihar ta su dake zaman shugaban masu rinjaye a majalisar jiha Honorabul Timothy Owoeye yana wanka a tsirara cikin jeji.

Haihuwar uwar sa: Matasa sun kama wani fitaccen dan siyasa yana wanka da jini tsirara

Haihuwar uwar sa: Matasa sun kama wani fitaccen dan siyasa yana wanka da jini tsirara
Source: Original

KU KARANTA: Buhari zai dauki sabbin ma'aikata 5,000

Shi dai shugaban masu rinjaye a majalisar jiha Honorabul Timothy Owoeye, an ce wankan da aka kama shi yana yi baya rasa nasaba da tsafi irin na 'yan tsubbu da kan sa 'yan siyasa yi musamman ma ganin zabukan 2019 na kara karatowa.

Legit.ng dai ta samu cewa matasan da suka kama shi sun ce dan majalisar yana tsakiyar wanka da jinin ne suka kama shi duk da dai kawo yanzu ba'a tabbatar da jinin mutane ne ba ko kuwa na dabba.

Da dan majalisar dai yaga dubun tasa ta cika shine ya baiwa matasan makudan kudade domin su rufa masa asiri amma daga baya kuma suka fallasa maganar.

A wani labarin kuma, Daya daga cikin manyan malaman addinin kirista a Najeriya dake zaman tsohon shugaban majami'un Pentecostal Fellowship of Nigeria (PFN), Dakta Mike Okonkwo ya bayyana cewa shi ba zai taba goyon bayan Inyamuri ya shugabancin Najeriya ba.

Dakta Mike ya yi wannan kalaman ne a lokacin da yake zantawa da wani babban malamin addinin kiristan kuma shugaban majami'un Redeemed Evangelical Mission (TREM), Victor Oluwasegun.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel