Ni Inyamuri ne, amma ba zan goyi bayan Inyamuri ya shugabanci Najeriya ba - Wani malamin Kirista

Ni Inyamuri ne, amma ba zan goyi bayan Inyamuri ya shugabanci Najeriya ba - Wani malamin Kirista

- Ba zan goyi bayan Inyamuri ya shugabanci Najeriya ba - Wani malamin Kirista

- Yace shi sake fasalin kasar yake so kawai ayi

Daya daga cikin manyan malaman addinin kirista a Najeriya dake zaman tsohon shugaban majami'un Pentecostal Fellowship of Nigeria (PFN), Dakta Mike Okonkwo ya bayyana cewa shi ba zai taba goyon bayan Inyamuri ya shugabancin Najeriya ba.

Ni Inyamuri ne, amma ba zan goyi bayan Inyamuri ya shugabanci Najeriya ba - Wani malamin Kirista

Ni Inyamuri ne, amma ba zan goyi bayan Inyamuri ya shugabanci Najeriya ba - Wani malamin Kirista
Source: Facebook

KU KARANTA: Jirgin kasa yayi hadari akan hanyar sa ta zuwa Abuja

Dakta Mike ya yi wannan kalaman ne a lokacin da yake zantawa da wani babban malamin addinin kiristan kuma shugaban majami'un Redeemed Evangelical Mission (TREM), Victor Oluwasegun.

Legit.ng ta samu cewa da yake karin haske game da ra'ayin nasa, ya bayyana cewa shi da inyamuri ya mulki Najeriya ya kwammace a sake fasalin kasar domin ta haka ne kadan yan kasar za su koma su gina yankin su.

A wani labarin kuma, Wasu matasa a jihar Osun dake a shiyyar kudu maso yammacin Najeriya sun cafke wani fitaccen dan siyasa a jihar ta su dake zaman shugaban masu rinjaye a majalisar jiha Honorabul Timothy Owoeye yana wanka a tsirara cikin jeji.

Shi dai shugaban masu rinjaye a majalisar jiha Honorabul Timothy Owoeye, an ce wankan da aka kama shi yana yi baya rasa nasaba da tsafi irin na 'yan tsubbu da kan sa 'yan siyasa yi musamman ma ganin zabukan 2019 na kara karatowa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel