Aiki dai: Shugaba Buhari zai sake daukar mutane 5,000 aiki a Najeriya

Aiki dai: Shugaba Buhari zai sake daukar mutane 5,000 aiki a Najeriya

- Shugaba Buhari zai sake daukar mutane 5,000 aiki a Najeriya

- Za'a dauke su ne a wata hukuma a Abuja

- Za suyi aikin kididdiga da tattara bayanai

Gwamnatin tarayyar Najeriya a karkashin shugabancin shugaba Muhammadu Buhari ta sanar da wasu shirye-shiryen ta na sake daukar akalla mutane dubu biyar aikin yi a hukumar tattara bayanai da kididdigar mazauna garin Abuja watau Basic Registry and Information System (BRISIN).

Aiki dai: Shugaba Buhari zai sake daukar mutane 5,000 aiki a Najeriya

Aiki dai: Shugaba Buhari zai sake daukar mutane 5,000 aiki a Najeriya
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Don Allah ku taimaka ku siya mun fom - Wani dan takarar Shugaban kasa

Shugaban hukumar dai ta BRISIN, Drakta Anthony Uwa, shine ya sanarwa da manema labarai hakan a garin na Abuja, babban birnin tarayya lokacin da yake zantawa da su.

Legit.ng ta samu cewa aikin na hukumar dai ya kunshi tattara bayanai tare da kuma kididdigar alkalumman al'amurran da suka shafi mazauna birnin da nufin tsara yadda gwamnati zata rika kasafta kudaden ta da kuma rarraba ayyukan ta.

A wani labarin kuma, Wasu matasa a jihar Osun dake a shiyyar kudu maso yammacin Najeriya sun cafke wani fitaccen dan siyasa a jihar ta su dake zaman shugaban masu rinjaye a majalisar jiha Honorabul Timothy Owoeye yana wanka a tsirara cikin jeji.

Shi dai shugaban masu rinjaye a majalisar jiha Honorabul Timothy Owoeye, an ce wankan da aka kama shi yana yi baya rasa nasaba da tsafi irin na 'yan tsubbu da kan sa 'yan siyasa yi musamman ma ganin zabukan 2019 na kara karatowa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel