Zaben 2019: Hukumar zabe ta hadu da babban cikas a majalisar tarayya

Zaben 2019: Hukumar zabe ta hadu da babban cikas a majalisar tarayya

- Hukumar zabe ta hadu da babban cikas a majalisar tarayya

- Yan majalisar sun dage ranar dawowar su

- Hakan na nufin karin dadewa kafin amincewa da kasafin kudin su

'Yan majalisar tarayyar Najeriya mun samu labarin cewa sun dage ranar dawowar su hutun da suka tafi daga 25 ga watan Satumba da muke ciki har zuwa cikin sati na biyu a cikin watan Oktoba mai kamawa.

Zaben 2019: Hukumar zabe ta hadu da babban cikas a majalisar tarayya

Zaben 2019: Hukumar zabe ta hadu da babban cikas a majalisar tarayya
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya siyo jirage 30 bayan hawan sa mulki

Wasu 'yan majalisar daga bangaren zauren dattawa da kuma wakilai da wakilin majiyar mu ya zanta da su sun bayyana cewa ranar dawowar ta su ta farko da suka sa kawo yanzu ta tabbata ba zata yiwuba .

Legit.ng ta samu cewa 'yan majalisar sun bayyana cewa a wannan lokacin da yawa daga cikin su ba za su samu damar dawowar ba saboda harkokin siyasa irin su zabukan fitar da gwani da suka rigaya suka soma kankama.

Wasu ma dai na ganin babu yadda za'ayi majalisar ta tabuka wani abu alhalin hankulan su duka yana a kan zabukan da ke gaban su a jam'iyyun su daban daban.

A wani labarin kuma, Yayin da zabukan shekarar 2019 ke ta kara karatowa, wasu masoyan dan takarar shugabancin kasar dake neman tikitin tsayawa a jam'iyyar adawa ta PDP, Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso sun yanka rago tare da addu'o'i ga Allah akan muradin na su.

Kamar yadda muka samu, masoyan na Kwankwaso da galibin su matasa ne sun fito ne daga karamar hukumar Kiru dake a jihar Kano inda kuma suka gudanar da Sallah da saukar al'qur'ani duk domin samun nasarar gwanin nasu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel