Da duminsa: Mayakan kungiyar Boko Haram sun bakunci kiyama bayan kai wa sojoji harin kwanton bauna

Da safiyar yau, Lahadi, ne dakarun rundunar soji ta 22 dake aikin kakkabe ragowar mayakan kungiyar Boko Haram a jihar Borno suka yi wani kazamin artabu da mayakan kungiyar Boko Haram.

Mayakan kungiyar ta Boko Haram ne suka fara kai wa dakarun sojin harin kwanton bauna yayin da suke kan hanyar su ta zuwa Bama daga Maiduguri.

Sai dai reshe ya juye da mujiya domin sojojin sun yi nasara a kan 'yan ta'addar bayan musayar wuta ta dan takaitaccen lokaci.

Dakarun sojin sun kashe dukkan mayakan kungiyar ta Boko Haram da suka kawo masu harin tare da kwashe dukkan makamansu.

Da duminsa: Mayakan kungiyar Boko Haram sun bakunci kiyama bayan kai wa sojoji harin kwanton bauna

Da duminsa: Mayakan kungiyar Boko Haram sun bakunci kiyama bayan kai wa sojoji harin kwanton bauna
Source: Twitter

DUBA WANNAN: An bawa hammata iska yayin rikicin shugabancin APC a Bauchi

Da duminsa: Mayakan kungiyar Boko Haram sun bakunci kiyama bayan kai wa sojoji harin kwanton bauna

Da duminsa: Mayakan kungiyar Boko Haram sun bakunci kiyama bayan kai wa sojoji harin kwanton bauna
Source: Twitter

Da duminsa: Mayakan kungiyar Boko Haram sun bakunci kiyama bayan kai wa sojoji harin kwanton bauna

Da duminsa: Mayakan kungiyar Boko Haram sun bakunci kiyama bayan kai wa sojoji harin kwanton bauna
Source: Twitter

Da duminsa: Mayakan kungiyar Boko Haram sun bakunci kiyama bayan kai wa sojoji harin kwanton bauna

Da duminsa: Mayakan kungiyar Boko Haram sun bakunci kiyama bayan kai wa sojoji harin kwanton bauna
Source: Twitter

A wani rahoton mai kama da wannan, amma a ranar Laraba 12 ga watan Satumba, Rundunar sojin Najeriya ta 145 da ke aikin tabbatar da zaman lafiya a Maiduguri (Ofireshon Lafiya Dole) sun yiwa wasu mayakan kungiyar Boko Haram da suka kai masu hari a sansaninsu kisan kiyashi.

Dakarun sojin sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram da dama tare da lalata makamansu masu yawa. Yanzu haka dakarun sojin na cigaba da farautar ragowar ‘yan mayakan Boko Haram din da suka tsere, kamar yadda Birgediya Texas Chukwu, darektan hulda da jama’a na hukumar soji, ya sanar ta shafin Kanal Sani Kukasheka Usman.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel