Dole APC ta ba ni dama in tafka muhawara da Shugaba Buhari – Moghalu

Dole APC ta ba ni dama in tafka muhawara da Shugaba Buhari – Moghalu

‘Dan takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar YPP ta Young Progressives Party watau Kingsley Moghalu ya bayyana cewa dole a kyale sa su gwabza muhawara da Shugaban kasa Muhammadu Buhari domin a san na zaba a 2019.

Dole APC ta ba ni dama in tafka muhawara da Shugaba Buhari – Moghalu

Moghalu yace ba za ta yiwu APC ta hana sa fuskar Buhari ba
Source: Instagram

Kingsley Moghalu wanda tsohon Mataimakin Gwamnan babban bankin CBN ne yayi wani jawabi a Legas lokacin da ya gana da ‘Yan jaridar Vanguard inda yayi alkawarin gyara kasar nan idan ya samu hawa kujerar Shugaban kasa.

‘Dan takarar Shugaban kasar yace ya kalubalanci Shugaba Buhari ya fito su yi mukabala kafin ayi zabe. Moghalu yace ba zai tsaya da Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo domin ba shi bane ‘Dan takarar Shugaban kasar APC.

Mista Kingsley Moghalu yace kamata yayi Yemi Osinbajo yayi mukabala tare da sauran masu neman kujerar Mataimakin Shugaban kasa. ‘Dan takaran yace ta tabbata cewa Buhari yana jin tsoron ya fito gaban Duniya yayi magana.

KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya tayi kokari wajen magance matsalar ambaliya

‘Dan takaran na Jam’iyyar YPP yace ba a jin Shugaba Buhari yayi magana sai lokacin da ya bar Najeriya. Moghalu yace idan Buhari ba zai iya ba gara yayi wa Jama’a bayani tun da wuri domin su sani amma Osinbajo ba zai tsaya masa ba.

Haka-zalika Moghalu ya nuna cewa idan ya zama Shugaban kasa ba zai bari ayi wargi ba domin kuwa kusan duk bayan ‘dan lokaci sai ya tsige Ministocin da ba su aiki a Gwamnatin sa domin ya gyarawa kowa zama a Gwamnati.

Kun dai ji cewa shi kuma Tsohon Shugaban kasa Jonathan yace PDP za ta lashe zaben 2019. A jiya Sule Lamido ya gana da Jonathan a gidan sa game da zaben 2019. Jonathan yace Lamido yayi kokarin lokacin da yayi mulki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel