Rt. Hon. Yakubu Dogara ya bayyana mafarar shigan sa harkar siyasa

Rt. Hon. Yakubu Dogara ya bayyana mafarar shigan sa harkar siyasa

Shugaban Majalisar Wakilai Rt. Hon. Yakubu Dogara yayi wata doguwar hira da Jaridar Daily Trust inda har bayyana yadda ya tsinci kan sa a harkar siyasa bayan da farko yana kyamar ta ainun.

Rt. Hon. Yakubu Dogara ya bayyana mafarar shigan sa harkar siyasa

Yakubu Dogara yace tsohon Gwamna Ahmad Muazu ya daura sa a hanya
Source: Twitter

Rt. Hon. Yakubu Dogara ya bayyana cewa da farko ya tsani siyasa saboda mugun yaudara da cin amanar da yake gani don haka ya zabi harkar kasuwanci. Sai dai da yake akwai abincin sa a nan, ya tsinci kan sa Majalisar Tarayya.

Dogara yace tsohon Gwamnan Bauchi watau Dr. Ahmadu Adamu Mu’azu ne yayi sanadiyyar sa fara shiga siyasa lokacin da ya nemi ya fito takarar Majalisa a 2007. Dogara yace a lokacin yayi kokarin yin gardama amma aka matsa masa.

KU KARANTA: Dogara ya fice daga APC zai koma Jam'iyyar PDP

Hon. Dogara ya bayyana cewa ba ya samun sukuni a Majalisa inda yace akalla duk rana ya kan tashi aiki ne wajen karfe 3:00 bayan ya gana da mutane kusan 30. Dogara yace Matar sa tana kewan sa domin ba shi da lokacin kan sa a yanzu.

Shugaban Majalisa Dogara yace ya fara koyarwa ne a wata Firamare bayan ya gama Makaranta a 1988. Daga baya kuma ya ajiye aiki ya koma Jami’a inda ya karanci ilmin shari’a inda yayi aiki har ya zama Mai ba wani Minista shawara a 2005.

Dogara ya godewa Ubangiji na irin nasarorin da ya samu inda ya kuma yabi tsohon Gwamnan Ahmad Muazu wanda yace har yanzu ba a kara samun irin sa a Jihar ba. Dogara yace a abinci yana da sha’awar tuwon accha da miyar taushe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel