Gwamnatin Tarayya ta fitar da N3bn domin magance annobar ambaliyar ruwa a Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta fitar da N3bn domin magance annobar ambaliyar ruwa a Najeriya

Mun samu rahoton cewa, cibiyar bayar da agaji na gaggawa ta NEMA, ta karɓi N3bn da gwamnatin tarayya ta fitar domin shawo kan lamari da kuma magance aukuwar annobar ambaliyar ruwa a kasar nan da ta zamto ruwa dare.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya bayyana, gwamnatin tarayya tayi gaggawar fitar da wannan makudan kudi a sakamakon gargadi da cibiyar binciken kimiya da fasaha ta fitar dangane da yiwuwa ta aukuwar annobar ambaliyar ruwa da ba za ta misaltu ba.

Shugaban cibiyar NEMA, Mista Mustapha Maihaja, shine ya bayar da wannan sanarwa cikin babban birnin kasar nan na tarayya, a yayin ganawarsa da dukkanin masu ruwa da tsaki kan hasashen aukuwar annobar da wani kwamiti ya gudanar da bincike cikin wasu jihohi na kasar nan.

Gwamnatin Tarayya ta fitar da N3bn domin magance annobar ambaliyar ruwa a Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta fitar da N3bn domin magance annobar ambaliyar ruwa a Najeriya
Source: Depositphotos

A cewar sa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da sahalewarsa ta fitar da wannan makudan kudi zuwa ga cibiyar domin daura damara gami da zama cikin shirin na magance annobar yayin auluwar ta.

Maihaja ya ke cewa, tuni cibiyar ta su ta bazama cikin aiki tukuru domin tunkarar wannan lamari a yayin da hasashe ke bayyana yiwuwa ta aukuwar ta cikin wasu jihohi na kasar nan.

KARANTA KUMA: Fadar Shugaban kasa ta bude wuta kan Bankin HSBC da ya yi hasashen rashin nasarar Buhari a zaben 2019

Yake cewa, binciken da kwamitin ya gudanar ya tabbatar da damuwar al'ummar wasu jihohi da tuni suka fara fuskantar wannan annoba da suka hadar da Neja, Kogi, Delta da kuma jihar Anambra.

Kazalika a makon da ya gabata ne jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, aukuwar ambaliyar ruwa ta salwantar da rayuka da dama da kuma asarar dukiya mai tarin yawa cikin wasu jihohi musamman na Arewa da suka hadar da; Kano, Kebbi, Jigawa da sauransu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel