Barazan kan rayuwar Atiku: PDP ta yiwa APC gugar zana

Barazan kan rayuwar Atiku: PDP ta yiwa APC gugar zana

- Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya koka kan cewar ana yiwa rayuwar sa da ta iyalinsa barazana saboda burinsa na son zama shugaban kasar Najeriya

- Jam’iyyar adawa ta PDP ta ce babu wanda zata tuhuma sai jam’iyyar APC mai mulki idan wani abu ya samu daya daga cikin ‘yan takarar ta

- PDP ta ce ba zata dauki zargin da Atiku ya yi da wasa ba tare da bukatar shugaba Buhari ya bayar da umarnin gudanar da bincike a kan lamarin

A cikin satin da muka yi bankwana da shi ne tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya koka kan cewar ana yiwa rayuwarsa da ta iyalinsa barazana saboda burinsa na son yin takarar shugaban kasa a zaben 2019.

Sai dai jam’iyyar adawa ta PDP ta ce babu wanda zata yi zargi idan ba jam’iyyar APC ba matukar wani abu ya samu daya daga cikin ‘yan takarar ta.

Barazan kan rayuwar Atiku: PDP ta yiwa APC gugar zana

Atiku
Source: Depositphotos

A jawabin da PDP ta fitar ta bakin Kola ologbondian, sakataren yada labarai na jam’iyyar, ta ce ba zata taba daukan batun barazana kan rayuwar Atiku da wasa ba tare da yin kira ga shugaba Buhari day a bayar da umarnin gudanar da bincike a kan dukkan koarfe-korafen da Atiku ya aike masa a rubuce.

Ologbondian ya bayyana cewar tuni jam’iyyar APC ta shiga halin dimuwa da damuwa saboda irin nagartar ‘yan takarar shugaban kasa da PDP ke da su tare da zargin gwamnati da yin amfani da ‘yan banga da jami’an tsaro domin kuntatawa ‘yan takarar ta.

DUBA WANNAN: Hotunan kauraye da maharba da suka dazukan Zamfara don farautar 'yan bindiga

Tun da jam’iyyar APC ta fahimci cewar dukkan ‘yan takarar mu sun fi karfin Buhari suka fara amfani da karnukan farauta a cikin hukumomin tsaro na gwamnati musamman ‘yan sanda, jami’an DSS da na hukumar EFCC domin firgita ‘yan takarar mu dake son yin takara a zaben 2019.

“Yanzu lamarin ya wuce amfani da karfin gwamnati har ya kai ga yin barazana a kan rayuwar ‘yan takarar mu. Muna son sanar da APC cewar babu abinda zai firgita mu ko ya saka tsoro a zukatanmu,” a cewar Ologbondian.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel