Karya ake min, garau da na ke - Tsohon gwamna Ladoja

Karya ake min, garau da na ke - Tsohon gwamna Ladoja

- Rashid Ladoja ya ce babu kanshin gaskiya cikin rahoton da aka wallafa na cewa ya yanke jiki ya fadi kana an garzaya dashi asibiti

- Tsohon gwamnan ya ce yana ganawa da wasu abokansa na siyasa lokacin da rahoton ya fara yaduwa

- Ladoja ya yi kira da jama'a suyi watsi da rahoton kuma tuni ya tuntubi kafar yada labaran da ta fara wallafa labarin

An samu dan majalisa dumu-dumu da laifin karyar yin aikin N41 a mazabar sa

An samu dan majalisa dumu-dumu da laifin karyar yin aikin N41 a mazabar sa
Source: Depositphotos

Tsohon gwamnan jihar Oyo, Rashidi Ladoja ya karyata rahotanin da ke yawa kafafen yadda labarai na cewa ya yanke jiki ya fadi kuma an garzaya dashi asbitin koyarwa na jami'ar Ibadan a safiyar yau.

Kafafen yadda labarai da dama sun wallafa labarin bayan sun samo rahoton daga wata kafar yadda labarai na yanan gizo.

DUBA WANNAN: Muhimman abubuwa 8 da ya kamata ku sani game da sabuwar Ministan Kudi, Zainab Ahmed

Cikin 'yan kwanakin nan Ladoja ya fice daga jam'iyyar PDP, ya koma jam'iyyar African Democratic Congress ADC kuma a yanzu yana daga cikin masu juya akalar sabuwar jam'iyyar a jiharsa har ma a tarayya.

Tsohon gwamnan da ya yi magana ta bakin hadiminsa na fanin yadda labarai, Lanre Latinwo, ya ce lafiyarsa kalau tun bayan dawowarsa daga yakin neman zaben dan takarar ADC na jihar Osun, Fatai Akinbade wadda akayi a jiya Alhamis.

Ya ce, "Rahoton ba gaskiya bane kuma mun tuntubi wanda ya fara yada jita-jitan. Ladoja yana ganawa da wasu abokan siyasarsa lokacin da rahoton ya fita. Yana nan lafiyarsa kalau kuma ba'a kai shi asibiti ba. Ya yi tafiya zuwa Abeokuta da Osun a ranar Alhamis kuma ya dawo lafiya. Babu kanshin gaskiya cikin rahoton."

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel