Rashin adalci: Wasu 'yan Najeriya sun yo ca akan Buhari game da sabbin nade-naden sa

Rashin adalci: Wasu 'yan Najeriya sun yo ca akan Buhari game da sabbin nade-naden sa

- Wasu 'yan Najeriya sun yo ca akan Buhari game da sabbin nade-naden sa

- Sun ce shugaba Buhari bai da adalci ko kadan

- Shugaban dai ya yi sabbin nade-nade 2 dukkan su daga arewa

Wasu 'yan Najeriya musamman ma daga bangaren kudancin kasar nan sun yi ta surutai da gungunai ga Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari game da sabbin nade-naden da ya yi a 'yan kwanakin nan.

Rashin adalci: Wasu 'yan Najeriya sun yo ca akan Buhari game da sabbin nade-naden sa

Rashin adalci: Wasu 'yan Najeriya sun yo ca akan Buhari game da sabbin nade-naden sa
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Jam'iyyar APC ta rabe 2 a jihar Taraba

Yan Najeriyar dai wadan da suka nuna rashin jin dadin su musamman ma a kafofin sadarwar zamani, sun bayyana nade-naden a matsayin babban rashin adalci da kuma tsantsar son kai daga bangaren na shugaban kasar da suka zarga da nada 'yan arewa kadai.

Legit.ng dai ta samu cewa a ranar Alhamis din da ta gabata ne shigaban kasar ya nada Yusuf Bichi wanda dan asalin jihar Kano ne a matsayin shugaban hukumar jami'an tsaron farin kaya na DSS.

A jiya kuma shugaban ya nada karamar ministar kudi da ta fito daga jihar Sokoto a matsayin babbar ministar kudin ta wucin gadi biyo bayan murabus din Kemi Adeosun.

A nasu bangaren, suma dai wasu 'yan arewar da dama sun nuna goyon bayan su ga shugaban kasar game da nade-naden inda suka ce ba laifi bane.

A wani labarin kuma, Daya daga cikin 'yan takarkarin kujerar shugaban kasar Najeriya a zabukan 2019 dake tafe mai suna Fela Durotoye, ya roki 'yan kasar da su taimaka masa su tattara masa kudin da zai sayi fom domin takarar tasa a jam'iyyar adawa ta Alliance for a New Nigeria (ANN).

Mun samu cewa fom din takarar shugabancin kasar na jam'iyyar adawar dai ana saida shi ne akan Naira miliyan 3.5 wanda ya bayar da shawarar cewa da an samu mutane kadan da kowa ya bayar da Naira dubu daya to za a hada masa kudaden fom din.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel