Zaben 2019: Bukola Saraki ya samu goyon bayan gwamnoni 6 don hambarar da Buhari

Zaben 2019: Bukola Saraki ya samu goyon bayan gwamnoni 6 don hambarar da Buhari

- Bukola Saraki ya samu goyon bayan gwamnoni 6 don hambarar da Buhari

- Cikin gwamnonin akwai gwamnan Kwara

- Cikin masu neman tikitin takara a PDP akwai Kwankwaso da Atiku

Wani labari da muke samu daga majiyar mu yana tabbatar mana da cewa shugaban majalisar dattawan Najeriya Sanata Bukola Saraki kawo yanzu ya samu goyon bayan akalla gwamnoni shida daga cikin sha hudu na jam'iyyar PDP a kokarin da yake yi na samun tikitin jam'iyyar.

Zaben 2019: Bukola Saraki ya samu goyon bayan gwamnoni 6 don hambarar da Buhari

Zaben 2019: Bukola Saraki ya samu goyon bayan gwamnoni 6 don hambarar da Buhari
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Matar babban sojan Najeriya da ya bace tayi magana

Duk da dai kawo yanzu bamu samu jerin sunayen gwamnonin ba, sai dai abun da muka tabbatar shine akwai na jihar sa ta Kwara, watau Abdulfatah Ahmad a cikin su.

Legit.ng ta samu cewa Sanata Bukola Saraki dake zaman tsohon gwamnan jihar Kwara, yanzu haka yana kasar Ghana wajen taron gangamin bizne tsohon shugaban majalisar dinkin duniya, Mista Kofi Anan.

Sauran wadanda ake sa ran za su iya zama ga Saraki din a wajen neman tikitin takarar shugabancin kasar a jam'iyyar PDP sun hada da gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal, Kwankwaso, Atiku da dai sauran su.

A wani labarin kuma, A wani labarin kuma, Daya daga cikin 'yan takarkarin kujerar shugaban kasar Najeriya a zabukan 2019 dake tafe mai suna Fela Durotoye, ya roki 'yan kasar da su taimaka masa su tattara masa kudin da zai sayi fom domin takarar tasa a jam'iyyar adawa ta Alliance for a New Nigeria (ANN).

Mun samu cewa fom din takarar shugabancin kasar na jam'iyyar adawar dai ana saida shi ne akan Naira miliyan 3.5 wanda ya bayar da shawarar cewa da an samu mutane kadan da kowa ya bayar da Naira dubu daya to za a hada masa kudaden fom din.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel