Rikita-Rikita: Jam'iyyar APC ta dare gida 2 a wannan jihar ta Arewa

Rikita-Rikita: Jam'iyyar APC ta dare gida 2 a wannan jihar ta Arewa

- Jam'iyyar APC ta dare gida 2 a jihar Taraba

- Uwar jam'iyya ta nada Ibrahim El-Suldi a matsayin shugaba

- Shi kuma Abdulmumuni Vaki yace bai san wannan ba

Labarin da muke samu yanzu ba da dadewa daga majiyar mu ta gidan jaridar Punch yana tabbatar mana da cewa jam'iyyar adawa a jihar Taraba dake a Arewa maso gabashin kasar nan ta APC ta rabe gida biyu.

Rikita-Rikita: Jam'iyyar APC ta dare gida 2 a wannan jihar ta Arewa

Rikita-Rikita: Jam'iyyar APC ta dare gida 2 a wannan jihar ta Arewa
Source: Twitter

KU KARANTA: Mutum 2 da ba barayi ba a gwamnatin Buhari

Wannan rikicin dai ya fito fili ne biyo bayan ranstsar da wani Malam Ibrahim El-Suldi a matsayin shugaban jam'iyyar ta APC da shugaban uwar kungiyar ta kasa Kwamared Adams Oshiomhole yayi a hedikwatar jam'iyyar a birnin Abuja.

Legit.ng ta samu cewa sai dai ba da dadewa ne ba sai wani mai suna Abdulmumuni Vaki yayi fatali da wannan nadin da akayi inda yayi ikirarin cewa shine halastaccen shugaban jam'iyyar a jihar kuma babu wanda ya isa ya sauke shi.

Haka ma dai Wani labari da muke samu daga majiyar mu yana tabbatar mana da cewa shugaban majalisar dattawan Najeriya Sanata Bukola Saraki kawo yanzu ya samu goyon bayan akalla gwamnoni shida daga cikin sha hudu na jam'iyyar PDP a kokarin da yake yi na samun tikitin jam'iyyar.

Duk da dai kawo yanzu bamu samu jerin sunayen gwamnonin ba, sai dai abun da muka tabbatar shine akwai na jihar sa ta Kwara, watau Abdulfatah Ahmad a cikin su.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel