Yan bindiga sun kashe mutane 2 tare da yin awon gaba da shanu 70

Yan bindiga sun kashe mutane 2 tare da yin awon gaba da shanu 70

- Wasu yan bindiga sun kashe mutane 2 tare da awon gaba da shanu 70

- Rundunar yan sanda ta jihar Filato ta tabbatar da hakan tana mai cewa lamarin ya afku ne a yammacin ranar Juma'a.

- Haka zalika, rundunar ta shawarci masu dabbobi a jiyar, da su kiyaye baiwa kananan yara kiwon dabbobinsu

Rundunar yan sanda ta bayyana cewa wasu yan bindiga sun kashe mutane biyu tare da yanka shanu 70 harnlahira a kauyen Turu, gudumar Kuru da ke a karamar hukumar Jos ta Kudu.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar da ke Filato, DSP Terna Tyopev, ya tabbatar da faruwar hakan a zantawarsa da manema labarai, ya ce harin ya afku ne a yammacin ranar Juma'a.

"Da misalin karfe 7 na yammacin ranar Juma'a, wani mazaunin kauyen Turu da ke a gundumar Kuru, karamar hukumar Jos ta Kudu, Mr Ezekiel Dalyop, ya kawo rahoton hakan ga ofishin rundunarmu na Vom, cewar wasu yan bindiga sun yi garkuwa da makiyaya guda uku tare da yin awon gaba da shanunsa guda 70.

"Da jin wannan rahoto muka garzaya yankin don kai dauki, inda muka samu nasarar kwato makiyayi daya daga cikin uku, mai suna Bitrus Joseph, mai shekaru 16 da haihuwa.

Da zafi zafi: Yan bindiga sun kashe mutane 2 tare da yin awon gaba da shanu 70

Da zafi zafi: Yan bindiga sun kashe mutane 2 tare da yin awon gaba da shanu 70
Source: Depositphotos

KARANTA WANNAN: Ya ragewa Dogara ya yi murabus ciki ruwan sanyi ko mu tsige shi ta tsiya - APC

"Rundunar mu ta musamman kan bincike, daga baya ta gano shanun da aka sace, sai dai a kokarin hakan, an kashe sauran makiyayan guda biyu, ma su suna; Meshack Dalton, mai shekaru 14, da kuma Pam Danjuma, mai shekaru 10.

"An gano gawar ta su a wani daji da ke kauyen Dahool Bob, a gundumar Kuru," a cewar sa.

Tyopev ya ce bayan gano gawarwakin, an kai su dakin ajiye gawa da ke cikin asibitin kirista na garin Vom.

Tyopev ya shawarci masu dabbobi a jihar da su kauracewa baiwa kananan yara kiwon dabbobinsu, don kaucewa faruwar irin wannan lamarin.

"A lokacin da muke yin ta'aziyya ga iyalan mamatan, muna kuma bukatar masu dabbobi a jihar, da su rinka baiwa mutane masu hankali kiwon dabbobinsu, wadanda za su iya hasaso idan akwai wani hadari da ke zuwa."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel