Ministan Kwadago ya bayyana lokacin da za ayi karin albashi

Ministan Kwadago ya bayyana lokacin da za ayi karin albashi

- Ministan Kwadago, Chris Ngige ya ce gwamnati za tayi karin albashin ma'aikata kafin zaben 2019

- Ngige ya fadi hakan ne bayan ya fito daga wata taro da shugaba Buhari da 'yan kwamitin inganta albashi na kasa

- Ya ce gwamnatin Buhari ta ma'aikata ne hakan yasa za tayi duk mai yiwuwa don ganin sun dara kafin zaben

Ministan Kwadago ya bayyana lokacin da za'a fara biyan sabuwar albashi

Ministan Kwadago ya bayyana lokacin da za'a fara biyan sabuwar albashi
Source: Depositphotos

Ministan Kwadago da Ayyuka na kasa, Chris Ngige, ya ce gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, tana kaunar ma'aikata hakan yasa za ta farantawa ma'aikatan Najeriya rai kafin babban zaben shekarar 2019.

Mr Ngige ya fadi hakan ne bayan ya fito daga wata taro da su kayi da shugaba Muhammadu Buhari da shugaban kwamitin inganta albashi mafi karanci a Najeriya, Amma Pepple.

DUBA WANNAN: Buhari ya yi hakuri da Saraki - Wata na hannun daman Obasanjo

A cewar Ministan, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, zaiyi wata ganawa da tawagar wata kungiya na tattalin arziki a ranar 18 ga watan Satumba inda za su cigaba da tattaunawa kan batun tsayar da albashi mafi karanci a Najeriya.

Ministan ya ce ba gaskiya bane ikirarin da wasu keyi na cewa gwamnatin shugaba Buhari na jan kafa saboda a cewarsa sunyi dukkan abinda ya kamata suyi.

"Wannan gwamnatin ta ma'aikata ce saboda haka dole zamu faranta musu rai kafin a gudanar da babban zabe; Mu 'yan gwargwarmaya ne saboda haka ba za mu juya musu baya ba," inji Ngige.

Ms Pepple, tsohuwar Shugaban ma'aikatan tarayya, ta shaidawa manema labarai cewa kwamitin ta zai mika rahotonsa a ranar 30 ga watan Satumba ko kuma kafin ranar.

Amma ta ce har yanzu gwamnati bata fadawa kwamitin adadin kudin da za ta iya biya a matsayin mafi karancin albashi ba amma abubuwa na tafiya kamar yadda ya kamata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel