Ya ragewa Dogara ya yi murabus ciki ruwan sanyi ko mu tsige shi ta tsiya - APC

Ya ragewa Dogara ya yi murabus ciki ruwan sanyi ko mu tsige shi ta tsiya - APC

- Jam'iyyar APC ta ce kamar yadda ta matsa lamba ga Sanata Bukola Saraki, shima Yakubu Dogara, dole ya yi murabus ko ta tsige shi ta tsiya

- Sakataren watsa labarai na APC, Nabena, Dogara ya dade yana nuna adawarsa ga ayyukan APC, wanda hakan ya kaishi ga aikata kuskuren sauya sheka zuwa PDP

- APC a shiyyar Kudu-maso-Kudu, tace kundin mulkin Nigeria bai baiwa marasa rinjaye jagoranci akan masu rinjaye a harkokin majalisa ba

Jam'iyyar APC ta ce kamar yadda ta matsa lamba ga shugaban majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki, shima kakakin majalisar wakilai ta tarayya, Yakubu Dogara, dole ya yi murabus da kashin kansa, ko kuma ya fuskanci shirin tsigewa daga kujerarsa da karfin tsiya.

A jerin gwanon zantawa ta wayar tarho da jaridar Punch ta ranar asabar, Sakataren jam'iyyar APC na kasa, Yekini Nabena da kuma mataiakim shugaban jam'iyyar a shiyyar Kudu-maso-Kudu, Hilliard Eta, sun ce tuni dama kakakin majalisar ya san abubuwan da zasu biyo baya ma damar ya koma PDP.

Nabena ya ce: "Lallai dole ne biri ya yi kama da mutum, dama Dogara ya dade yana nuna adawarsa ga ayyukan APC, wanda hakan ya kaishi ga aikata kuskuren sauya sheka zuwa PDP.

KARANTA WANNAN: Yanzu yanzu: Tsohon gwamnan jihar Osun ya yanke jiki ya fadi, an garzaya da shi asibiti

"Ya zama kakakin majalisar ne saboda a lokacin shi mamba ne na jam'iyyarmu, duk da cewa mu bai sanar da mu cewa ya sauya sheka ba, amma tunda yanzu an bayyana ficewarsa, abu mafi sauki kuma da ya dace a gareshi shine ya yi murabus daga kujerarsa ta kakakin majalisa."

Ya ragewa Dogara ya yi murabus ciki ruwan sanyi ko mu tsige shi ta tsiya - APC

Ya ragewa Dogara ya yi murabus ciki ruwan sanyi ko mu tsige shi ta tsiya - APC
Source: Twitter

Shima da ya ke magana makamanciyar wannan, Eta ya ce tsarin kundin mulkin Nigeria bai baiwa jam'iyyar marasa rinjaye ta zama jagora ga jam'iyyar masu rinjaye a harkokin majalisa ba. Ya bayyana cewa ba dai dai ba ne ace marasa rinjaye su zamo suna shugabantar masu rinjaye.

Ya ce: "Bawai bukatar wadanda suka zauna suka tsara kundin mulkin Nigeria ace wai wani mamba daga jam'iyyar marasa rinjaye a majalisu dokoki na tarayya a ce wai shi ne ya ke jagorantar masu rinjaye ba.

"Ya zama wajibi mu tsige su gana daya kuma zasu riga rana faduwa a kotu. Wannan umurni ne daga jam'iyyarmu zuwa ga mambobin jam'iyyar da ke a majalisar wakilai da kuma ta dattijai, da su tsige Saraki da Dogara."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel