An kashe wani basarake yayin da ya ke aiki a gonarsa

An kashe wani basarake yayin da ya ke aiki a gonarsa

- Hukumar 'yan sanda na jihar Ekiti ta sanar da rasuwar wani basarake a garin Ijero Ekiti mai suna Adewole Ajayi

- Ajayi ya rasu ne sakamakon harbinsa a cinya da wani Ojo-Aro ya yi yayin da ya kama shi yana masa sata a gona

- Binciken 'yan sanda ya bayyana cewa Ojo-Aro ya dade yana yiwa mutane sata a gonakinsu a kauyukan da garinsu

Hukumar 'yan sanda ta sanar da cewa an kashe wani babban basarake, Adewole Ajayai, a gonarsa da ke garin Ijero Ekiti da ke karamar hukumar Ekiti a jiya Juma'a.

Ana zargin wani mutum mai suna Dele Ojo-Aro wanda gonarsa ke kusa da gonar basaraken wanda akafi sani da Iroko Ekiti ne ya kashe shi a cikin gonar bayan ya kama shi yana satar masa doya da sanyin safiya.

An kashe wani basarake yayin da ya ke aiki a gonarsa

An kashe wani basarake yayin da ya ke aiki a gonarsa
Source: Twitter

Tuni jami'an 'yan sanda sum cafke wanda ake zargi da kisan basaraken.

DUBA WANNAN: Muhimman abubuwa 8 da ya kamata ku sani game da sabuwar Ministan Kudi, Zainab Ahmed

Kakakin hukumar 'yan sandan jihar, DSP Caleb Ikechukwu ya ce binciken da suka fara yi ya nuna cewa wanda ake zargin gagararen barawo ne wanda ya saba zuwa gonakin mutane yana musu sata.

"Kwakwarar majiya ta tabbar mana cewa wanda ake zargin ya tafi gonar marigayin domin satar doya, amma da mai gonar ya iso ya yi kokarin kama shi sai ya harbe shi da bindigar mafarauta a cinya," inji Ikechukwu.

Sarkin garin Iroko Ekiti, Oba Sunday Ekundayo shima ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Wanda ake zargi da aikata kissan dan asalin garin Odo Oro Ekiti ne wadda ke makwabtaka da Ijero Ekiti inda aka kashe marigayin.

Afkuwar wannan lamarin ya jefa gaba tsakanin mazauna kauyukan guda biyu kamar yadda wata majiya ta ce.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel