Sarkin Sakkwato, Sultan Abubakar, naso ayi gyara a harkar koyar da fida

Sarkin Sakkwato, Sultan Abubakar, naso ayi gyara a harkar koyar da fida

- A kokarin da ake na inganta harkar kiwon lafiya a kasar nan, Sarkin Musulmi yayi magana kan kyautata harkar

- A ziyarar da suka kai masa, sun kuma bashi uban tafiya a lamarin harkar kungiya

- Sun kai ziyarar ban girma ne a fadar sa

Sarkin Sakkwato, Sultan Abubakar, naso ayi gyara a harkar koyarwa

Sarkin Sakkwato, Sultan Abubakar, naso ayi gyara a harkar koyarwa
Source: Depositphotos

Kungiyar masana kan harkar tiyata ta fida, watau Anatomical Society of Nigeria, ASN, ta kaiwa sarkin Musulmi ziyarar ban girma a fadar mulkinsa dake Sokkoto, ya kumma tarbe su hannu bibiyu.

Sun kai ziyarar ban girma ne a fadar sa, a ziyarar da suka kai masa, sun kuma bashi uban tafiya a lamarin harkar kungiya. A kokarin da ake na inganta harkar kiwon lafiya a kasar nan, Sarkin Musulmi yayi magana kan kyautata harkar.

A nasa jawabin, Sarki Abubakar, yayi kira ga kungiyar da ma'aikatan, dasu kara zage damtse don inganta harkar aikinsu, da ma inganta tsarin ilimin a kasar nan baki daya.

DUBA WANNAN: Dole 'yansanda su rage tumbinsu

Shugaban kungiyar na duniya baki daya, wanda dashi aka kai ziyarar, Professor Beverley Kramer, yayi godiya ga Sarki, kan yadda ya jajirce kan harkar ilimin kimiyya musamman ma karatun mata wadanda sai dasu harkar ilimin ke ci gaba.

Kungiyar sun kuma ba bayyana farin cikinsu da godiya da irin gudummawar da dattijon ke bayarwa a harkar ta ilimi da kiwon lafiya a fadin kasar nan sannan sun bashi mukamin uban tafiya a harkar ASN ta kasa baki daya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel