EFCC ta aike wa Fayose wasika kan ranar da take so ya kawo kansa

EFCC ta aike wa Fayose wasika kan ranar da take so ya kawo kansa

- Hukumar EFCC ta amsa wasikar da gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya aike mata

- Fayose ya fadawa EFCC cewa zai kawo kansa ofishin hukumar domin amsa tambayoyi a ranar 16 ga watan Oktoba, kwana daya bayan ya sauka daga mulki

- Amma a amsar da EFCC ta aike masa, ta ce ya kawo kansa ranar 20 ga watan Satumba

Bayan gwamna Ayodele Fayose na jihar Ekiti ya rubuta wasika ga Hukuma Yaki da Rashawa EFCC inda ya ce zai amsa gayyatar hukumar a ranar 16 ga watan Oktoba, hukumar ta amsa wasikarsa amma ta ce ya kawo kansa ranar Alhamis 20 ga watan Satumba.

Nigerian Tribune ta ruwaito cewa EFCC ta gayyaci Fayoce ne saboda ya amsa wasu tambayoyi da suka shafi shi a cikin wata bincike da hukumar ke gudanarwa.

EFCC ta aike wa Fayose wasika, kan ranar da take so ya kawo kansa

EFCC ta aike wa Fayose wasika, kan ranar da take so ya kawo kansa
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Buhari ya yi hakuri da Saraki - Wata na hannun daman Obasanjo

Legit.ng ta gano cewa a wasikar da ya aike wa EFCC a ranar 10 ga watan Satumban 2018, gwamnan ya ce zai kawo kansa a ranar 16 ga watan Oktoba domin amsa dukkan tambayoyin da suke bukatar yi masa.

A wasikar ta EFCC ta aike masa a ranar 13 ga watan Satumba mai dauke da sa hannun Direktan Ayyuka, Umar Abba Mohammed a madadin Shugaban riko na hukumar, Ibrahim Magu, hukumar ta bukaci gwamnan ya bayyana a ranar 20 ga watan Satumba kuma ta tabbatar masa ba za ta keta hakkin kariya da doka ta bashi ba.

EFCC ta mika godiyarta ga Fayose saboda irin hadin kai da ya bata na niyyar amsa gayyatar da tayi masa domin kashin kansa saboda biyaya ga dokan kasa.

Idan ba'a manta ba, Fayose ya dade yana gwagwarmaya da EFCC kuma sun shiga kotu sau da yawa saboda wasu bincike da ake gudanarwa kan kudaden da gwaman ya mallaka na kashin kansa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel