Yawan 'yansanda masu tumbi ya fara yawa - shugaban hukumar ya koka

Yawan 'yansanda masu tumbi ya fara yawa - shugaban hukumar ya koka

- Sai an horar dasu tare da jarabawa kafin karin girma

- Da ana ma yan sanda karin girma kara zube

- Dole ne jami'i yayi shekaru 2 zuwa 3 kafin a kara mishi girma

Yawan 'yansanda masu tumbi ya fara yawa - shugaban hukumar ya koka

Yawan 'yansanda masu tumbi ya fara yawa - shugaban hukumar ya koka
Source: Depositphotos

Kwamishin hukumar 'yansanda (Police Service Commission) tace daga yanzu bazata karawa jami'i matsayi ba tare da yayi horarwa da jarabawa ba.

Hakan ya fito daga shugaban yada labarai da hulda da jama'a, Ikechukwu Ani, yace shugaban kwamishan, Musiliu Smith ne ya bayyana hakan a wani taro 'yansanda a ranar juma'a a Abuja.

"Daga yanzu, daya daga cikin ka'idojin karin girma shine cin Jarabawar hukumar, " Yace.

DUBA WANNAN: Soyayya ta sa ya bata qodarsa

Mista Smith yace "a baya dai hukumar tana karawa jami'an girma ne ba tare da sun samu halartar horarwa sabon matsayin da aka kaisu ba."

"Daga yanzu, dole a hada sakamakon horarwa tare da bukatar karin girma ga hukumar,"

Mista Smith yace dole ne a bar jami'i yayi shekaru 2 zuwa 3 a matsayi kafin a fara tunanin kara masa girma. Ya nuna damuwar shi akan yanda jami'an Police Mobile Force (PMF) suke dadewa ba tare da karin girma ba. Yayi kira da dena hakan.

Ya shawarci duk wani jami'in Dan sanda ya samu takardun tuki,domin bukatar gaggawa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel