Laifin da ake zargin Kemi Adeosun dashi bai tsaya a murabus ba, harda kurkuku

Laifin da ake zargin Kemi Adeosun dashi bai tsaya a murabus ba, harda kurkuku

- Jita-jita ta zama gaskiya

- Kemi Adeosun ta ajje aiki

- An zarge ta da qaga satifiket

Laifin da ake zargin Kemi Adeosun dashi bai tsaya a murabus ba, harda kurkuku

Laifin da ake zargin Kemi Adeosun dashi bai tsaya a murabus ba, harda kurkuku
Source: Depositphotos

A dokar Najeriya, idan aka sami mutum da laifin da aka zarge shi dashi bayan anje kotu, hukuncinsa yana kamawa daga taara, ko dri ko duka biyu, ko takunkumai.

Zargin da ake wa Kemi Adeosun na qage ne, watau ta coga takardar cewa tayi bautar kasa ko an yaffe mata, bayan kuma ya cancanta tayi din.

Muddin aka kaita kotu, kkuma aka same ta da wannan laifi, to fa kurkuku zata je ta zauna zaman wasu shekaru, sai dai in shugaban kasa ya yafe mata.

Ita dai tayi karatu da aiki ne a kasashen waje, Ingila, inda aka haife ta, amma ta dawo Najeriya ne domin ta taimaka.

DUBA WANNAN: Zaman gidan kurkuku kan basarake

Ba'a dai sa rai gwamnatin Tarayya zata kai ta kotu kan wannan batu, barinta gwamnati ma yazo musu da bambarakwai ne.

Ta dai iya aiki, babu ja, amma irin wannan zargi kan hana mutum aiki, musamman ganin ance wannan rashin takarda ya sa wadanda suka sani suna ta saka ta ta iyar musu da nufinsu na samun kudaden gwamnati zuwa ofishinsu ba bisa qa'ida ba.

Za dai muso ace ko wadanda suka titsiye ta ta basu kudade zata iya tona wa domin suma a tuhume su.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel