Dramar da aka tafka bayan fage kan murabus din Kemi Adeosun

Dramar da aka tafka bayan fage kan murabus din Kemi Adeosun

- Ajiye aikin da Kemi Adeosun tayi bai zo a saukake ba

- Ta fara shirye shirye ne tun ranar laraba

- An shawarce ta data aje aikin ta ne don kare ragowar nagartar ta

Dramar da aka tafka bayan fage kan murabus din Kemi Adeosun

Dramar da aka tafka bayan fage kan murabus din Kemi Adeosun
Source: Facebook

Ajiye aikin da ministan kudi, Kemi Adeosun, tayi a ranar juma'a bai zo a saukake ba. Ajiye aikin ya biyo bayan bincike mai tsanani ne, tun bayan da ya bayyana cewa takardar bautar kasar ta ta bogi ce.

Mai bada shawara na musamman ga shugaban kasa akan labarai, Femi Adesina ya tabbatar da hakan a yammacin juma'a. Ya sanar da cewa shugaban kasar ya amince da ajiye aikin da ministan tayi. Ya kuma bayyana abinda wasikar ta kunsa.

A ranar 7 ga watan yuli ne muka samu rahoton cewa ministan ta tsallake bautar kasa kuma ta mallaki takardar bogi domin rufe hakan. Duk da korafe korafen yan Najeriya, Mrs Adeosun ta yi tsit.

Jami'an NYSC aka so hada baki dasu don rufe zancen amma hakan yaci tura tunda Suleiman Kazaure ya kasa tankwaruwa. Ya tabbatar da cewa babu abinda shi da jami'an shi zasu iya yi.

DUBA WANNAN: Pauline Tallen nason zama sanata

Wani bangare na jami'an gwamnati ya zamo abin bai musu dadi ba amma shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya tabbatar da cewa zai yi bincike kafin yanke hukunci. Wanda hakan ya dau satika da yawa.

A ranar laraba ne ta fara shirin barin aiki bayan da Abba kyari ya sanar da ita cewa ta kawo takardar aje aikin ta, shawara ce daga shugabancin kasa domin tattala ragowar nagartar ta.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel