Yan bindiga sun kashe mutane 8 a jihar Nasarawa

Yan bindiga sun kashe mutane 8 a jihar Nasarawa

Rundunar yan sandan Najeriya reshen jihar Nasarawa a ranar Juma’a, 14 ga watan Satumba ta tabbatar da kisan mutane takwas da wasu yan bindiga suka yi a kauyen Sofiyo dake karamar hukuar Toto dake jihar.

Kakakin yan sandan jihar, Kennedy Idrisu, ya tabbatar da lamarin ga kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a Toto.

Yace da dama sun ji mummunan rauni daga harin.

Yan bindiga sun kashe mutane 8 a jihar Nasarawa

Yan bindiga sun kashe mutane 8 a jihar Nasarawa
Source: Depositphotos

Mista Idrisu ya shawarci mutane da su tabbatar da cewa sun kai rahoton duk wani rikici ga hukumomin da suka dace maimakon sanya hannu cikin rikicin.

Yace rundunar ba zata yi sanya ba wajen magance duk wani aikin assha da hukunta masu laifi ba.

Ya kuma kalubalanci mazauna yankin das u kai karar duk wani da suka ga ya taka doka domin a hukunta shi.

KU KARANTA KUMA: Sarkin Ogoni ya nada wa Shugaba Buhari sarauta

A baya Legit.ng ta rahoto cewa a kokarin rundunar sojin Najeriya na kara inganta tare da karfafa harkar tsaron kasar da kuma samun jami’ai masu jini a jika, rundunar ta sake yaye wasu sabbin dalibai matasa 1,558 wadanda suka hada da mata da maza.

Bikin yaye daliban wanda aka gudanar a yau Juma’a, 14 ga watan Satumba a cibiyar horar da sojoji na Kaduna, ya samu halartan shugaban hafsan soji, Air Marshal Sadique Abubakar, a matsayin babban bako.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel