Hadiman shugaba Buhari tana son kwace kujerar Ekweremadu

Hadiman shugaba Buhari tana son kwace kujerar Ekweremadu

- Hadiman shugaba Buhari, Juliet Ibekaku-Nwagwu ta yanki tikitin takarar Sanata a jam'iyyar APC

- Ibekaku-Nwagwu za ta fafata da mataimakin shugabam majalisar dattawa, Ike Ekweremadu a zaben na 2019

- Ibekaku-Nwagwu ta ce ta fito takarar ne domin amsa kirar mutanen ta na yankin Enugu ta Yamma da suka ce sun gaji da wakilcin Ekweremadu

Mai taimakawa shugaban kasa na musamman kan gyare-gyare Shari'a, Mrs Juliet Ibekaku-Nwagwu ta sanar da niyyarta na tsayawa takarar Sanata a yankin Enugu ta Yamma karkashin inuwar jam'iyyar APC.

Rahottani sun bayyana cewa mataimakin shugabam majalisar dattawa, Ike Ekweremadu, da ke wakiltan yankin na Enugu ta Yamma shima ya bayyana niyyarsa ne sake tsayawa takarar a 2019 karkashin jam'iyyar PDP.

Wata na hannun daman Buhari ta dau alwashin kwace kujerar Ekweremadu

Wata na hannun daman Buhari ta dau alwashin kwace kujerar Ekweremadu
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Wani Sanata ya bukaci kotu ta aika Saraki gidan yari

Ibekaku-Nwagwu ta bayyanawa manema labarai niyyarta na takarar ne a jiya Alhamis a garin Enugu inda ta ce musu tuni har ta cika fom din tsayawa takarar kuma ta mayar ofishin APC da ke Abuja.

A cewarta, ta fito takarar ne domin amsa kiran da matasa da mata da maza har ma da wasu kungiyoyin siyasa a yankin su kayi mata na shiga takarar.

Ta ce mutanen sun koka da irin sallon wakilcin da Ekweremadu ya keyi inda su ka ce ba'a samu wata cigaba na azo-a-gani a yankin ba.

Ibekaku-Nwagwu ta ce ta amsa kiran mutanen ta daga kananan hukumomi biyar wanda suka hada da Aninri, Agwu, Ezeagu, Oji River and Udi domin maye gurbin Ekweremadu.

"Abinda suke bukata shine ababen more rayuwa da zai basu damar gudanar da ayyukansu kamar yadda ya kamata," inji hadimar shugaban kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel