Kwamishina ya ajiye mukaminsa, ya fice daga PDP a jihar Taraba

Kwamishina ya ajiye mukaminsa, ya fice daga PDP a jihar Taraba

- Kwamishinan sadarwa na jihar Taraba, Anthony Danbram ya sauya sheka daga PDP zuwa APGA

- Mr Danbram ya ce ya fice daga PDP ne saboda rashin adalcin da jam'iyyar ke masa ta hanyar hana shi tiktin takara

- Ciyaman din APGA na jihar, Ishaya Boko ya yi maraba da Danbram kuma ya yi alkawarin tallafa masa ya cimma burinsa

Kwamishinan Sadarwa na jihar Taraba, Anthony Danbram ya yi murabus daga mukaminsa sannan ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar All Progressive Grand Alliance, (APGA) domin ya cimma burinsa na tsayawa takara.

Mr Danbram ya sanar da ficewarsa daga PDP da kuma murabus dinsa daga gwamnatin gwamna Ishaku Darius ne a yau Juma'a a sakatariyar APGA yayin da yake karbar katinsa na jam'iyyar saboda ya zama cikaken dan jam'iyya.

Kwamishina ya ajiye mukaminsa, ya fice daga PDP a jihar Taraba

Kwamishina ya ajiye mukaminsa, ya fice daga PDP a jihar Taraba
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: 2019: Dan takarar shugaban kasa ya bukaci a dakatar da Buhari

A cewarsa, rashin adalcin da jam'iyyar PDP tayi masa saboda ya nuna yana son yin takarar majalisar wakilai na jiha a yankin Lai yasa ya fice daga jam'iyyar saboda ya koma wata jam'iyya ya yi takarar.

"Na tattauna da magoya baya na a ranar Laraba kuma sun bukaci in koma wata jam'iyyar wadda ba PDP ba kuma za su cigaba da bani goyon baya.

"A yau na zabi jam'iyyar APGA, jam'iyyar mu itace za ta zama jam'iyya na farko a karamar hukumar Lau saboda a baya na gina jam'iyya kuma yanzu zan gina APGA a karamar hukumar Lau," inji Danbram.

A jawabinsa na karbar Danbram, Ciyaman din jam'iyyar APGA na jihar, Ishaya Bako ya tabbatarwa tsohon kwamishinan cewa jam'iyyar za ta mara masa baya domin ya cimma burinsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel