Hukumar EFCC ta sha alwashin hukunta jami'anta da suka kai sumame bankin Standard Chartered

Hukumar EFCC ta sha alwashin hukunta jami'anta da suka kai sumame bankin Standard Chartered

- Hukumar EFCC ta sha alwashin hukunta wasu jami'anta da suka kai sumame a Bankin Standard Chartered a jihar Legas

- Hukumar ta ce sumamen da wasu sanye da kayan EFCC suka kai, na iya zama aikin wasu bata garin jami'an hukumar da ke aiki ba tare da izini ba

- Uwujaren ya kuma shaida cewa labarin da ake yadawa na cewar hukumar ta cafke babban manajan bankin, kanzon kurege ne

Hukumar da ke yaki da masu yiwa dukiyar jama'a zagon kasa EFCC ta sha alwashin yin bincike kan sumamen da wasu jami'anta suka kai Bankin Standard Chartered a jihar Legas, tana mai cewa jami'an da suka kai sumamen zasu fuskanci hukuncin hukumar.

Wilson Uwujaren, mai magana da yawun hukumar, ya bayyana jakan a wata sanarwa jim kadan bayan da aka kai sumamen.

Legit.ng ta ruwaito yadda wasu jami'an hukumar ta EFCC ta kai sumame a bankin a ranar Juma'ar nan.

Sai dai Uwujeren ya ce wadanda suka kai sumamen sun yi gaban kansu ne, ba da sanin hukumar ba.

KARANTA WANNAN: Da dumi dumi: An karyata rahotannin da ke yawo na cewar Kemi Adeosun ta yi murabus

Shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu

Shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu
Source: Depositphotos

"Biyo bayan bukatun yan jaridu na son sanin gaskiyar lamarin kai sumame da wasu jami'an hukumarmu suka yi a bankin Standard Chartered a yau 14 ga watan Satumba, hukumar na sanar daukacin jama'a cewa babu masaniyar hukumar akan wannan sumame," a cewar sa.

"Sumamen da wasu sanye da kayan EFCC suka kai, na iya zama aikin wasu bata garin jami'an hukumar da ke aiki ba tare da izini ba.

"Wannan sumamen ya saba dokoki da tsarin gudanar da ayyukan hukumar, kuma ba salon hukumar bane yin sumame kai tsaye ga bankuna ko hukumomin da ke tu'ammali da kudade ba tare da izini ba.

"Akan gayyaci shuwagabannin bankuna da hukumomin da hukumar EFCC zata bincika, don yi masu tambayoyi bayan kammala bincike. A tsawon shekarun nan, bankuna na bada hadinnkai wajen gabatar da shuwagabannin su ga hukumar don bincike."

Uwujaren ya kuma shaida cewa labarin da ake yadawa na cewar hukumar ta cafke babban manajan bankin, kanzon kurege ne.

Wannan sumame ya faru makwanni biyu bayan da babban bankin Nigeria ya bayyana sunan bankin Standard Chartered tare da wasu bankuna uku, bisa laifin bayar da takardar CCIs a madadin masu saka hannun jari na kamfanin MTN, ba bisa ka'ida ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel