Sauya sheka: Yan majalisar wakilai sun sha alwashin ba Dogara kariya daga tsigewa

Sauya sheka: Yan majalisar wakilai sun sha alwashin ba Dogara kariya daga tsigewa

- Mambobin majalisar wakilai wakilai sun sha alwashin ba Dogara kariya daga tsigewa

- Ana rade-radin cewa Shugaban APC na kasa na yunkurin tsige kakakin majalisar wakilan

- Dogara dai ya sauya sheka daga APC zuwa PDP

Mambobin majalisar wakilai karkashin kwamitin Parliamentary Democrats Group (PDG) a ranar Juma’a, 14 ga watan Satumba sun kaddamar da cewar zasu zuba ido sosai sannan su shiryya kare martaba da yancin kakakin majalisar wakilai, Hon. Yakubu Dogara aka duk wani baraza kan sauya shekarsa daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki zuwa Peoples Democratic Party (PDP).

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa daga kakakin kungiyar Hon. Timothy Golu zuwa ga manema labarai a Abuja a jiya, Alhamis, 13 ga watan Satumba.

Sauya sheka: Yan majalisar wakilai sun sha alwashin ba Dogara kariya daga tsigewa

Sauya sheka: Yan majalisar wakilai sun sha alwashin ba Dogara kariya daga tsigewa
Source: Twitter

Yan majalisan sun sha alwashin cewa zasu dakile duk wani yunkuri na cin mutuncin kakakin majalisar ko wani dan majalisa don kawai ya zabi yin takara ta jam’iyyar PDP.

A halin yanzu, Jam’iyyar APC mai mulki ta rasa gaba daya shugabancin Majalisun Tarayyar Najeriya bayan da Shugaban Majalisar Wakilai na kasar Rt. Hon. Yakubu Dogara ya koma PDP.

KU KARANTA KUMA: Zan dawo da Najeriya kan turban inganci idan aka zabe ni a matsayin shugaban kasa - Kwankwaso

A jiya ne Shugaban Majalisar Wakilai ya bi Takwaran sa Bukola Saraki zuwa PDP. Dogara ya sanar da ficewar sa daga APC ne ta bakin wani babban Hadimin sa Turaki Hassan Dogara yace APC ba addini ba ce da za ayi riko da ita.

Yakubu Dogara ya tsere daga APC zuwa Jam'iyyar PDP ne bayan da wasu ‘Yan Mazabar sa ta Bogoro/Dass/Tafawa Balewa su ka saya masa fam din takara a karkashin Jam’iyyar PDP su na rokon sa alfarma yayi watsi da APC ya huta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel