Jihar Legas: Faduwar wata babbar tanka ta janyo rufe hanyar Ikorodu

Jihar Legas: Faduwar wata babbar tanka ta janyo rufe hanyar Ikorodu

- Sakamakon faduwar wata babbar tanka da ta yi barin sinadarin da take dauke da shi, an rufe zirga zirga akan titin har sai an kammala magance matsalar

- Hukumar kwana kwana ta jihar Legas, ta sanar da rufe hanyar, tare da shawartar matafiya da su nemi wata hanyar

Hukumar ta kuma shaida cewa akwai jami'an kai daukin gaggawa da ke aiki a inda tankar ta fadi, don gujewa tashin gobara a wajen

Sakamakon faduwar wata babbar tanka dauke da sinadarin da ake gaurayawa da man fetur, a titin Ikorodu da ke jihar Legas, inda kuma ta yi barin sinadarin akan titin, an rufe zirga zirga akan titin har sai zuwa lokacin da aka kammala magance matsalar.

Tankar, wacce ta fadi a yankin Kosofe da ke a Ketu, ta janyo cunkoson ababen hawa musamman ga mazauna jihar ta Legas da ke dawowa daga Ikorodu.

KARANTA WANNAN: Da dumi dumi: An karyata rahotannin da ke yawo na cewar Kemi Adeosun ta yi murabus

Hukumar kwana kwana ta jihar Legas, ta sanar da rufe hanyar, tare da shawartar matafiya da su nemi wata hanyar, zuwa lokacin da za'a kammala magance matsalar.

Jihar Legas: Faduwar wata babbar tanka ta janyo rufe hanyar Ikorodu

Jihar Legas: Faduwar wata babbar tanka ta janyo rufe hanyar Ikorodu
Source: Twitter

"Idan har kana dawowa daga Ikorodu,Mile 12, Kosefe. To ka sani an rufe hanyar na wani lokaci, sakamakon faduwar wata babbar tanka mai dauke da sinadarin da ake gaurayawa da man fetur," a cewar hukumar, ta shafinta na Twitter.

Hukumar kwana kwanan ta kuma shaida cewa akwai jami'an kai daukin gaggawa da ke aiki a inda tankar ta fadi, don gujewa tashin gobara a wajen.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel