2019: APC Bauchi sun jero dalilai 2 da suka sanya su lamuncewa Buhari da Gwamna Abubakar

2019: APC Bauchi sun jero dalilai 2 da suka sanya su lamuncewa Buhari da Gwamna Abubakar

- Jam'iyyar APC a Bauchi ta amince da tsayar da Shugaba Buhari da Gwamna Abubakar a matsayin yan takaranta

- Sun ce sun gamsu da irin ayyukan ci gaba da tsaro da suka samar a fadin kasar da jihar

- Jam'iyyar tace zata yi amfani da wakilai ne wajen zaben yan takaran ta

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Bauchi ta lamuncewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan jihar, Mohammed Abubakar a matsayin yan takaran Shugaban kasa da na gwamna a zaben 2019, kamfanin dillancin labarai ta rahoto.

Abubakar Al-Saddiqque, kakakin gwamnan, ya bayyana a wata sanarwa a Bauchi a ranar Juma’a, 13 ga watan Satumba, cewa jam’iyyar ta yanke shawarar ne a wani taron masu ruwa da tsaki a ranar Alhamis, 14 ga watan Satumba, a gidan gwamnati.

Al-Sadique yace ganawar sun kuma tabbatar da cewa jam’iyyar ta yanke shawarar yin zaben fidda gwani na amfani da wakilai a zabukan 2019. “An yanke shawarar ne duba ga tarin ci gaba da zaman lafiya a kasar da jihar Bauchi.

"Akwai ci gaba sosai a lamarin tsaro da ci gaban albarkatun kasa a karkashin wannan gwamnati mai albarka” inji shi.

2019: APC Bauchi sun jero dalilai 2 da suka sanya su lamuncewa Buhari da Gwamna Abubakar

2019: APC Bauchi sun jero dalilai 2 da suka sanya su lamuncewa Buhari da Gwamna Abubakar
Source: Twitter

Yace sun yi amanna kan cewa gwamnatin APC ta taba rayuwar talakawa don haka suka yarje ma gwamnan da shugaban kasar.

Yace mutanen jihar Bauchi sun ji dadin jajaircewar shugaban kasa da gwamnan wajen yaki da ta’addanci da sauran ayyukan assha.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa dan takaran shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Rabiu Kwankwaso, yayi alkawarin magance lamarin tsaro a kasar idan har aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a 2019.

KU KARANTA KUMA: An kama mutane 2 da suka yi garkuwa da gawa domin neman kudin fansa N5m

Kwankwaso ya dau wannan alkawari ne a ranar Juma’a, 14 ga watan Satumba, a Makurdi lokacin da ya jagoranci mambobin Kwankwasiyya a ziyarar taya murna ga Gwamna Samuel Ortom.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel