Yanzu Yanzu: Shugaban ma'aikata na kasa ta saka labule da Kemi Adeosun

Yanzu Yanzu: Shugaban ma'aikata na kasa ta saka labule da Kemi Adeosun

Mun samu daga Daily Nigerian cewa shugaban ma'aikata na kasa, Winifred Oyo-ita da gana da ministan kudi, Kemi Adeosun a yau Juma'a.

Ba'a san takamamen dalilin ganawar ta su ba amma wata majiyar ta ce ganawar ba za ta rasa nasaba da batun zancen yin murabus din ministan da wasu kafafen yadda labarai suka wallafa.

Wata kwakwarar majiya ta tabbatarwa Daily Nigerian cewa Oyo-ita ta isa ofishin Adeosun tun misalin karfe 9 na safiyar yau a yayin da ministan kudin ta cigaba da karbar wasu baki.

Yanzu Yanzu: Shugaban ma'aikata na kasa ta saka labule da Kemi Adeosun

Yanzu Yanzu: Shugaban ma'aikata na kasa ta saka labule da Kemi Adeosun
Source: UGC

DUBA WANNAN: Wani Sanata ya bukaci kotu ta aika Saraki gidan yari

"Tana ofishinta tun karfe 9 na safiyar yau. Ta gana da shugaban ma'aikata na kasa da wasu baki da suka kawo mata ziyara.

"Bisa ga dukkan alamu abubuwa ba dai-dai suke tafiya ba amma munyi mamakin ganin ta tana cigaba da ayyukan ta kamar yadda ta saba," inji majiyar da ke ma'aikatar kudi.

A cewar majiyar, abin mamaki kawai shine ministan ba ta hallarci taron kwamitin zartarwa na FEC da aka gudanar a ranar Laraba da ta gabata.

Majiyar kuma ta ce gwamnonin jihohin Kebbi da Zamfara sun ziyarci Ministan Kudin a ranar Laraba, bayan haka gwamnan jihar Kebbi ya sake dawowa ofishin ministan a ranar Alhamis inda suka kwashe sa'o'i uku suna ganawa.

Rahotanni sun ce Ministan mai shekaru 51 tayi murabus a yau sakamakon korafe-kofare da ake yi bayan an gano cewa tana amfani da takardar sallamar hidimar kasa ta bogi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel