Zan dawo da Najeriya kan turban inganci idan aka zabe ni a matsayin shugaban kasa - Kwankwaso

Zan dawo da Najeriya kan turban inganci idan aka zabe ni a matsayin shugaban kasa - Kwankwaso

- Kwankwaso yace Najeriya na da isasshen kudin da za’a iya amfani dashi waje kare al’umman ta

- Yayi alkawarin magance lamarin tsaro a kasar idan har aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a 2019

- Sanata Shehu Sani ya kaddamar da cewa babu makawa Buhari zai lashe zaben 2019

Dan takaran shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Rabiu Kwankwaso, yayi alkawarin magance lamarin tsaro a kasar idan har aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a 2019.

Kwankwaso ya dau wannan alkawari ne a ranar Juma’a, 14 ga watan Satumba, a Makurdi lokacin da ya jagoranci mambobin Kwankwasiyya a ziyarar taya murna ga Gwamna Samuel Ortom.

Kamfanin dillanci labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa Ortom ya sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa Peoples Democratic Party (PDP) a kwanakin baya.

Zan dawo da Najeriya kan turban inganci idan aka zabe ni a matsayin shugaban kasa - Kwankwaso

Zan dawo da Najeriya kan turban inganci idan aka zabe ni a matsayin shugaban kasa - Kwankwaso
Source: Twitter

Dan takarar shugaban kasar ya bayyana cewa kasar na da isasshen kudin da za’a iya amfani dashi waje kare al’umman ta.

A cewarsa Najeriya kasa ce da aka fi daraja shanu sama da dan Adam.

KU KARANTA KUMA: An yi garkuwa da gawa domin neman kudin fansa

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Sanata mai wakiltan yankin Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana cewa duk da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gaza magance wasu lamura, zai yi nasarar lashe zaben 2019.

Da yake Magana a shirin Politics Today na gidan talbijin din Chennels, Sani yace shugaban kasar ya cimma wasu nasarori da zai sa ya iya lashe kuri’un yan Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel