Da dumi dumi: An karyata rahotannin da ke yawo na cewar Kemi Adeosun ta yi murabus

Da dumi dumi: An karyata rahotannin da ke yawo na cewar Kemi Adeosun ta yi murabus

- Ana kyautata zaton cewa rahotannin da ake yadawa na cewar ministar kudi Mrs Kemi Adeosun ta yi murabus, na iya zama kanzon kurege

- Wani babban hadimin ministar, wanda ya ce a boye sunansa, ya ce Sam wannan batu ba gaskiya bane

- Daraktan watsa labarai, Mr Hassan Dodo, ya ce ba shi da wata masaniya na cewar Adeosun ta sauka daga mukaminta na ministar kudi

Ana kyautata zaton cewa rahotannin da ke yawo a kafafen watsa labarai na yanar gizo, dama kafafen sada zumunta na zamani, da ke nuni da cewa ministar kudi Mrs Kemi Adeosun ta yi murabus daga wannan mukami nata a ranar Juma'a, na iya zama kanzon kurege.

Tun bayan da wata kafar watsa labarai ta yanar gizo ta buga labarin ajiye aikin Adeosun daga ministar kudi, sauran kafafen watsa labarai na yanar gizo suka dauki rahoton, wanda ya mamaye ko ina cikin kankanin lokaci.

Sai dai, kamfanin jaridar yanar gizo na Tribune wanda ya ke a ma'aikatar har zuwa karfe 3:35 na yamma, ya tabbatar da cewa babu wata alama da ke nuna cewa ministar ta yi murabus daga mukaminta.

KARANTA WANNAN: Yanzu Yanzu: Shugaban kasa Buhari ya karbi bakuncin shuwagabannin yankin Ogoni

Da dumi dumi: An karyata rahotannin da ke yawo na cewar Kemi Adeosun ta yi murabus

Da dumi dumi: An karyata rahotannin da ke yawo na cewar Kemi Adeosun ta yi murabus
Source: Depositphotos

Wani babban hadimin ministar, wanda ya ce a boye sunansa, ya ce: "Sam wannan batu ba gaskiya bane"

"Idan kun fahimta zaku ga cewa babu wata sanarwa dangane da lamarin tun farkon tasowarsa a ranar 7 ga watan Satumba, dangane da cewar takardar shaidar bautar kasa ta ministar jabu ce.

"Wannan kawai suna son cimma wata manufa ce, kuma ba zamu taimaka masu wajen tabbtar da hakan ba. Gani nan dai tare da ku, kuna iya ganin sauran hadimai dama jami'an tsaro kowa yana aikinsa.

"Hatta ita kanta ministar tana ofishinta tana gudanar da ayyukanta. Kada ku yarda da rahotannin karya da ake yadawa a yanar gizo," a cewar hadimin.

KARANTA WANNAN: Yanzu yanzu: An yi awon gaba da mata masu yawa a sabon harin Adamawa

Legit.ng ta tattara rahoton cewa ayyuka na ci gaba da tafiya yadda suke kamar kullum a ofishin ministar ba tare da wata alama da zai nuna cewa Adeosun ta yi murabus ba.

Daraktan watsa labarai, Mr Hassan Dodo, ya ce ba shi da wata masaniya na cewar Adeosun ta sauka daga mukaminta na ministar kudi.

Wani babban jami'i a ma'aikatar, wanda shima ya bukaci a boye sunan sa, ya ce babu kamshin gaskiya a cikin wannan labarin, illa dai jita jita da wasu marasa kishin kasa suke yadawa don cimma bukatun kawunansu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel