Matasa sun gudanar da gangami tare da karaɗe jihar Imo domin nuna goyon bayan su ga Shugaba Buhari

Matasa sun gudanar da gangami tare da karaɗe jihar Imo domin nuna goyon bayan su ga Shugaba Buhari

A yau Juma'a Babbar rana, dubunnan matasa sun gudanar da gangami domin bayyana goyon bayan sa karara kan kudirin shugaba kasa Muhammadu Buhari na sake neman tsayawa takarar kujerarsa kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito.

Rahotannin sun ruwaito cewa, bayyana goyon bayan ta hadar har da mamemin takarar kujerar gwamnan jihar kuma tsohon shugaban ma'aikata na gwamnan jihar, Ugwumba Uche Nwaso.

Matasan sanye da riguna masu dauke da hotunan Buhari na Nwaso, sun karade tare da shawagin manyan hanyoyi dake babban birnin jihar na Owerri tare da karaji da kururuwa wake ta sai Baba.

Sai dai abin takaici wannan lamari ya janyo cuzguni ga al'ummar jihar a sakamakon tsaikon hada-hada gami da dakile al'amurran da harkoki a jihar musamman yadda jerin gwamnon motoci su ka tsayar da jihar wuri guda.

Matasa sun gudanar da gangami tare da karaɗe jihar Imo domin nuna goyon bayan su ga Shugaba Buhari

Matasa sun gudanar da gangami tare da karaɗe jihar Imo domin nuna goyon bayan su ga Shugaba Buhari
Source: Depositphotos

A yayin tarba gami da lale maraba da wannan dandazo na matasa a shelkwatar jam'iyyar APC ta jihar, Nwosu ya yabawa wannan hobbasa tare da mika godiyarsa a gare su gami da bayar da tabbacinsa na shimfida tsare-tsare da za su samar da ayyuka a jihar.

KARANTA KUMA: A dandalan sada zumunta kadai ake hangen ƙurar jam'iyyar PDP - Keyamo

Ya kuma yabawa matasan musamman dangane da goyon bayan kudirin shugaba Buhari na tazarce, tare da cewar wannan ita kadai ce hanya matabbaciya da al'ummar kabilar Ibo za su mulki kasar nan a shekarar 2023.

'Dan takarar gwamnan ya kuma sha alwashi ga matasan akan inganta duk wani jin dadi da kuma walwala muddin ya yi nasarar lashe kujerar gwamnan jihar a yayin babban zabe na 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel