An kama mutane 2 da suka yi garkuwa da gawa domin neman kudin fansa N5m

An kama mutane 2 da suka yi garkuwa da gawa domin neman kudin fansa N5m

- Yan sandan jihar Imo sun cafke wasu mutane biyu

- An kama su ne bayan sunyi garkuwa da gawar wata dattijuwa domin karban kudin fansa

- Wadanda ake zargin dai sun sace gawat tsohuwar ne daga dakin ajiye gawa na wani asibiti

Jami’an yan sanda sun yi ram da wasu mutane biyu da ake zargi da garkuwa da gawar wata tsohuwa a yankin kudu maso gabashin kasar.

Rundunar yan sandan Owerri babban birnin jihar Imo, sun bayyana cewa mutanen sun yi garkuwa da gawar ne daga wajen ajiye gawa a wani asibiti, sannan kuma suka kai ta daji.

Bayan haka sai suka bukaci a biya naira miliyan hudu a matsayin kudin fansa daga asibiti da kuma iyalan marigayiyar, cewar yan sanda.

An yi garkuwa da gawa domin neman kudin fansa

An yi garkuwa da gawa domin neman kudin fansa
Source: Twitter

An cafke wadanda ake zargin, wadanda a baya aka taba samu da laifi, a wani samamen da aka kai musu.

Tuni dai akai damka gawar ga iyalan marigayiyar.

KU KARANTA KUMA: Gwamna Dankwambo ya caccaki masu sauya shekar da suka yasar da PDP a 2015

Kwanan nan aka sako mutanen daga gidan yari bayan sun yi zaman kaso bisa laifin garkuwa da mutane.

A wani lamari makamanci haka, Legit.ng ta rahoto cewa wasu mutane da ake zargin makiyaya ne sun yi awon gaba da mata a wani hari da suka kai kauyukan Gwon, Bolki da Nzumosu a karamar hukumar Numan da ke jihar Adamawa.

Garuruwan da ke cikin karamar hukumar Numan na ci gaba da fuskantar hare hare tun daga farkon watan Janairun wannan shekarar, hare haren da hukumomi ke kallon ya zarce a kirashi da rikicin makiyaya da manoma.

Da ta ke tabbatar da faruwar harin, yar majalisa mai wakiltar mazabar Numan a majalisar dokoki ta jihar, Misis Sodom Tayedi ta shaidawa manema labarai cewa makiyayan na ci gaba da mamaye sauran garuruwan da ke makwaftaka da su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel