Ta bayyana: Ashe Buhari ne ya umurci Kemi Adeosun ta tafi

Ta bayyana: Ashe Buhari ne ya umurci Kemi Adeosun ta tafi

Duk da cewan sai yau Juma’a ta bayyana, Shugaba Buhari ya yanke shawaran Sallamar minister kudi, Kemi Adeosun. Sahara Reporters ta samu rahoto.

Majiyoyi biyu masu inganci na kusa da gwamnati sun bayyanawa Sahara Reporters cewa Kemi Adeosun tayi murabus da gaske amma Buhari ya dade da koranta.

Abinda yasa aka bayyana murabus dinta a yau shine korafe-korafen da wasu ke yi kan nadin sabon shugaban hukumar DSS, Yusuf Magaji. Yan kudancin Najeriya suna korafin cewa Buhari ya cire dan kudu domin maye gurbinsa da dan Arewa.

Majiyar tace: “Mun samu labari tun karfe 7 na safe cewa Buhari ya salami Adeosun,”.

Gabanin yanzu, Jaridar Premium Times matsawa ministar kudi, Kemi Adeosun, lambar murabus bisa ga zargin amfani da takardan bautan kasa bogi.

KU KARANTA: Ministan kudi, Kemi Adeosun, ta yi murabus

Ministan kudi wacce aka haifa kuma tayi karatu a kasar Ingila ba tayi bautar kasan Najeriya wanda ya wajabta kan ko wani dan Najeriyan da ya kammala karaunsa jami'arsa kasa da shekaru 30.

Adeosun maimakon yin bautar kasa, ta sayi takardar shaidan daga hannun wasu domin gabatarwa majalisar dattawa lokacin da shugaba Buhari ya nadata minista a gwamnatinsa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel