Siyasa: Adams Oshiomole ya fara kaidin tsige Dogara

Siyasa: Adams Oshiomole ya fara kaidin tsige Dogara

- An fara yiwa kakakin majalisar wakilai barazanar tsigeshi daga kujerarsa

- Shugaban majalisar ya lashi takobin tsige Bukola Saraki ko ta kaka, an dawo kan Dogara

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Adams Aliyu Oshiomole, ya fara shirye-shiryen tsige kakakin majalisar wakilar, Yakubu Dogara, daga kujerarsa.

Wata majiyata bayyanawa jaridar Cable cewa Oshiomole ya fara tattaunawa da mambobin jam’iyyar, musamman yan majalisan wakilai kan yadda za’a cire Dogara.

Majiyar ta kara da cewa shugaban jam’iyyar ya dauki wannan mataki bayan rahoton sauya shekar Dogara zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

KU KARANTA: Ministan kudi, Kemi Adeosun, ta yi murabus

Har yanzu, kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara bai bayyana fitarsa daga jam’iyyar APC ba duk da cewan yana musharaka cikin harkokinsu.

A watan Agusta, ya ki halartan taron masu ruwa da tsakin jam’iyyar APC da akayi a Abuja.

A zaben majalisar dattawan mazabar jihar Bauchi ta kudu, jam’iyyar PDP ta lashe kuri’un karamar hukumar Yakubu Dogara, Bogoro.

Siyasa: Adams Oshiomole ya fara kaidin tsige Dogara

Siyasa: Adams Oshiomole ya fara kaidin tsige Dogara
Source: UGC

Tun daga lokacin aka fara zargin Yakubu Dogara da yiwa jam’iyyar APC zagon kasa tunda tsoron kada a tsigeshi kawai ya hanashi sauya sheka lokacin da abokan aikinsa suka koma jam’iyyar PDP.

Tun daga lokacin majalisar dokokin tarayya ta ki dawowa bakin aiki. Yayinda majalisa ke shirin dawowa kafin karshen wata Satumba, jam’iyyar APC ta shirya tsaf domin tsige shugaban majalisar dattawa da na wakilai tunda sunfita daga jam’iyyar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel