A dandalan sada zumunta kadai ake hangen ƙurar jam'iyyar PDP - Keyamo

A dandalan sada zumunta kadai ake hangen ƙurar jam'iyyar PDP - Keyamo

Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, kakakin kungiyar yakin neman zabe ta shugaban kasa Muhammadu Buhari, Mista Festus Keyamo, ya mayar da da martani ga jam'iyyar adawa ta PDP kan sukar Ubangidansa.

Mista Keyamo ya yi martaninsa zuwa ga jam'iyyar PDP dangane da sukar shugaba Buhari da a cewar ta ya dakile kwararar romon dimokuradiyya cikin jam'iyyar sa ta APC kasancewar sa dan takara daya tilo da jam'iyyar za ta fitar a matsayin gwani.

Yake cewa, sabanin yadda jam'iyyar PDP ta fitar da fam din takara daya rak ga tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan a shekarar 2015 da ta gabata, jam'iyyar APC ta fitar da fam din takara ga dukkan mabukata illa iyaka da suka zabi janyewa shugaba Buhari a sakamakon mashahurancin sa a kasar nan.

A dandalan sada zumunta kadai ake hangen ƙurar jam'iyyar PDP - Keyamo

A dandalan sada zumunta kadai ake hangen ƙurar jam'iyyar PDP - Keyamo
Source: Facebook

A yayin ci gaba da mayar da martani ga jam'iyyar, Mista Keyamo ya kuma bayyana cewa, jam'iyyar PDP a halin ta banu ta lalace da ba bu inda take iya wata fuffuka ko tayar da kura face a zaurukan sada zumunta.

KARANTA KUMA: Ba bu wata rashin jituwa tsakani na da Obasanjo - Atiku

Legit.ng ta ruwaito cewa, a ranar Alhamis din da ta gabata ne jam'iyyar PDP da sanadin kakakin ta Mista Kola Ologbondiyan, ya kalubalanci jam'iyyar APC dangane da tsayar da shugaba Buhari a matsayin dan takara daya tilo na jam'iyyar.

Mista Kola ya kuma bayyana cewa, wannan lamari shike kara haskaka damar jam'iyyar PDP lallasa shugaba Buhari a yayin babban zabe na 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel