Babu wani abu da zai iya hana Buhari cin zaben 2019 – Shehu Sani

Babu wani abu da zai iya hana Buhari cin zaben 2019 – Shehu Sani

- Sanata Shehu Sani yace babu wani abu da zai iya hana Buhari cin zaben 2019

- Sani yace duk da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gaza magance wasu lamura, zai yi nasara

- Ya kuma ce sukar da PDP ke yima Shugaban ba zai hana shi lashe zaben ba

Sanata mai wakiltan yankin Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana cewa duk da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gaza magance wasu lamura, zai yi nasarar lashe zaben 2019.

Da yake Magana a shirin Politics Today na gidan talbijin din Chennels, Sani yace shugaban kasar ya cimma wasu nasarori da zai sa ya iya lashe kuri’un yan Najeriya.

Legit.ng ta tattaro cewa, Sani yace baya shakku kan cewa Buhari zai lashe zaben shugaban kasa na 2019 bisa ga nasarorin da ya samu a shekaru uku da suka gabata.

Babu wani abu da zai iya hana Buhari cin zaben 2019 – Shehu Sani

Babu wani abu da zai iya hana Buhari cin zaben 2019 – Shehu Sani
Source: Depositphotos

Sani ya kuma bayyana cewa sukar gwamnatin shugaban kasar da jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party ke yawan yi ba zai shafi nasarar Buhari a zabe mai zuwa ba.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa dan takarar kujeran shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Gwamna Hassan Ibrahim Dankwambo, ya caccaki yan siyasan da suka dawo jam’iyyar gabannin zaben 2019.

KU KARANTA KUMA: Ba bu wata rashin jituwa tsakani na da Obasanjo - Atiku

Dankwambo, gwamnan jihar Gombe kuma dan takaran kujerar shugaban kasa a jam’iyyar ya wallafa wata tambaya a shafinsa na twitter a ranar Alhamis, 13 ga watan Satumba cewa, da ace dukkanin mambobin jam’iyyar sun barta a 2015 da yanzu za’a samu jam’iyyar da har za’a dawo a yanzu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel