Gwamna Dankwambo ya caccaki masu sauya shekar da suka yasar da PDP a 2015

Gwamna Dankwambo ya caccaki masu sauya shekar da suka yasar da PDP a 2015

- Gwamna Hassan Ibrahim Dankwambo, ya caccaki yan siyasan da suka dawo jam’iyyar gabannin zaben 2019

- Yace da ace dukkaninsu sun yasar da PDP a 2015 da babu jam'iyya har yanzu

Dan takarar kujeran shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Gwamna Hassan Ibrahim Dankwambo, ya caccaki yan siyasan da suka dawo jam’iyyar gabannin zaben 2019.

Dankwambo, gwamnan jihar Gombe kuma dan takaran kujerar shugaban kasa a jam’iyyar ya wallafa wata tambaya a shafinsa na twitter a ranar Alhamis, 13 ga watan Satumba cewa, da ace dukkanin mambobin jam’iyyar sun barta a 2015 da yanzu za’a samu jam’iyyar da har za’a dawo a yanzu.

Koda yake gwaamnan bai ambaci sunan kowa ba a jawabinsa, amma hasashe sun nuna cewa babu mamaki hannunka mai sanda yake yi ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da kuma Gwamna Tambuwal na jihar Sokoto wadanda suka sauya sheka zuwa PDP kwanan nan kuma suka sanya ran mallakar tikitin takaran kujerar shugaban kasa na jam’iyyar.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana cewa ba bu wata rashin jituwa mai tsanani dake tsakanin sa da tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo, sabanin yadda ake ikirari a kasar nan.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Ministan kudi, Kemi Adeosun, ta yi murabus

Atiku ya yi wannan karin haske ne cikin birnin Lokoja na jihar Kogi yayin ganawa da manema labarai a shelkwatar jam'iyyar sa ta PDP a ranar Alhamis din da ta gabata.

Tsohon Mataimakin shugaban kasar ya ziyarci jihar ne a yayin ci gaba da shawagin sa da karade jihohin kasar nan domin neman goyon baya tare da neman samun shiga kan kudirin sa na hankoron kujerar shugaban kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel