Yanzu Yanzu: 'Yan bingida sun kai hari wasu kauyuka a jihar Adamawa

Yanzu Yanzu: 'Yan bingida sun kai hari wasu kauyuka a jihar Adamawa

Wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton makiyaya ne sun kai hari wasu kauyuka uku a jihar Adamawa inda suka kone gidaje masu yawa.

Channels tv ta ruwaito cewa garuruwan da aka kai harin sun hada da Gon, Bolki da Nzomosu da ke karamar hukumar Numan da ke jihar Adamawa.

Dan majalisar tarayya mai wakiltan mazabar Numan, Hon. Sodom Tayedi, ya shaidawa manema labarai a yau Juma'a cewa 'yan bindigan sun kai harin ne misalin karfe 7 na safiyar yau Juma'a.

Yanzu Yanzu: 'Yan bingida sun kai hari wasu kauyuka a jihar Adamawa

Yanzu Yanzu: 'Yan bingida sun kai hari wasu kauyuka a jihar Adamawa
Source: Facebook

DUBA WANNAN: An cafke wani matashi yayin da yake lalata allon takarar Buhari (hotuna)

Ya ce 'yan bindigan sun rika harbe a iska sannan suka bankawa gidajen jama'a wuta, hakan ya sanya juma'a suka bar gidajensu domin neman inda zasu fake.

A halin yanzu ba'a tabbatar da mutanen da suka rasu sakamakon harin ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel