Ba bu wata rashin jituwa tsakani na da Obasanjo - Atiku

Ba bu wata rashin jituwa tsakani na da Obasanjo - Atiku

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana cewa ba bu wata rashin jituwa mai tsanani dake tsakanin sa da tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo, sabanin yadda ake ikirari a kasar nan.

Atiku ya yi wannan karin haske ne cikin birnin Lokoja na jihar Kogi yayin ganawa da manema labarai a shelkwatar jam'iyyar sa ta PDP a ranar Alhamis din da ta gabata.

Tsohon Mataimakin shugaban kasar ya ziyarci jihar ne a yayin ci gaba da shawagin sa da karade jihohin kasar nan domin neman goyon baya tare da neman samun shiga kan kudirin sa na hankoron kujerar shugaban kasa.

Turakin na Adamawa na daya daga cikin jiga-jigan 'yan takara 12 dake hankoron kujerar shugaban kasa karkashin inuwa ta jam'iyyar PDP.

Ba bu wata rashin jituwa tsakani na da Obasanjo - Atiku

Ba bu wata rashin jituwa tsakani na da Obasanjo - Atiku
Source: Depositphotos

Atiku ya bayyana cewa, ba bu wata matsananciyar rashin jituwa dake tsakanin sa da tsohon Ubangidansa, inda ya ce za su sulhunta duk wani sabani dake tsakanin su da zarar ya samu sahalewar tsayawa takara a jam'iyyarsa ta PDP.

KARANTA KUMA: Mayakan wani reshe na Boko Haram sun kashe Shugabansu, Mamman Nur

Ya kuma kalubalanci jam'iyyar APC dangane da rikon sakainar kashi da ta yiwa kasar nan musamman ta fuskar gurbacewar tattalin arziki da kuma rashin aikin yi da ya yi tsanani a tsakanin matasa.

Kazalika yayin ziyarar neman goyon baya da kai jihar Kano a ranar Larabar da ta gabata, Atiku ya sha alwashin inganta ci gaban kasar nan ta kowace fuska muddin ya samu nasarar cimma birin zuciyar sa na kasancewa shugaban kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel