Dogara ya fadi sharadi daya da zai sa ya cigaba da zama a APC

Dogara ya fadi sharadi daya da zai sa ya cigaba da zama a APC

- Kakakin majalisar tarayya, Yakubu Dogara ya ce a shirye yake ya yi sulhu a APC amma ba za'a tursasa shi zuwa rokon tikiti ba

- Dogara ya kuma ce yana son jam'iyyar APC ta yiwa wasu 'yan majalisa da aka mayar saniyar ware adalci

- Dogara ya kuma ce magoya bayansa sune tikitin sa shi yasa baya fargaban zaiyi nasara a duk jam'iyyar da ya tafi

Kakakin majalisar wakilai na tarayya, Honarabul Yakubu Dogara, ya ce yana ta tabbas cewa mutanen mazabarsa za su jefa masa kuri'a ba tare da la'akari da jam'iyyar da ya ke takara a karkashinta ba.

Kakakin majalisar da ake kyautata tsamanin ya koma jam'iyyar adawa ta PDP ya yi wannan furucin ne yayin da yake karbar magoya bayansa da suka kai masa ziyara a gidansa da ke babban birnin tarayya, Abuja.

Dogara ya fadi sharadi daya da zai sa ya cigaba da zama a APC

Dogara ya fadi sharadi daya da zai sa ya cigaba da zama a APC
Source: Twitter

Ya kuma bayyana cewa an umurci ya tafi ya roki tikitin takara a jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

DUBA WANNAN: APC ta bayyana abinda zai faru da Dogara idan ya koma PDP

"Na yi shawarar ba zanyi takara ba. Sai aka ce min za'a bani tikiti a APC amma sai na tafi na roka. Ni kuma na ce bana bukatar tikitin domin a siyasa ban taba zuwa gidan kowa rokon tikitin takara ba.

"Magoya baya na sune tikiti na. Na fada musu cewa ka jam'iyyar zero nayi takara, mutane na za su kada min kuri'a. Idan dai ana zance yankunan Bogoro/Dass/Tafawa Balewa ne ko a wace jam'iyya nayi takara zanyi nasara da izinin Allah."

Dogara ya ce wannan ba itace gwagwarmayarsa ta farko a siyasa ba kuma ya yi nasara a baya kuma wannan ma zaiyi nasara. Ya ce babu wanda zai masa barazana ko kuma ya hana shi takarar zabe a jam'iyyar da aka gina tare da shi.

Da yake tsokaci kan batun sulhu, Dogara ya ce ba zai karba tikitin APC ba har sai jam'iyyar ta yiwa wasu 'yan majalisar adalci, 'yan majalisar da ya lissafa sun hada da Sanata Suleiman Nazif, Sanata Isa Hamma Misau, Hon. Ahmed Yarima, Hon. Aminu Tukur da Maryam Bagel.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel