Paparoman Katolica ya amshi takardar barin aikin wani limami da yake wa yara fyade

Paparoman Katolica ya amshi takardar barin aikin wani limami da yake wa yara fyade

- An sami karin koke koken limaman coci na yi wa yara fyade

- An zargi coci da danne labaan don kawai a fita kunya

- Wannan karon dubban yara abin ya shafa

Paparoman Katolica ya amshi takardar barin aikin wani limami da yake wa yara fyade

Paparoman Katolica ya amshi takardar barin aikin wani limami da yake wa yara fyade
Source: Depositphotos

Paparoma Janho na yanzu, Francis, ya amince wa wani limami da shi yi murabus, saboda an same shi da laifin lalata da qananan yara da iyayensu suka kawo ajiya coci domin a koyar dasu ikilisiya a can kasar Amurka.

Badakalar, ba ita ce ta farko ba, a kasashen duniya inda cocin tayi ta kokarin rufa-rufa kan lamarin.

Kasashe da yawa sun ma haramta irin wannan dabi'a ta mikawa limamai yara domin suyi almajirta a mujami'u, ga limamai wadanda sun haramtawa kansu da kansu aure, duk da kuwa sha'awar saduwa tana ga kowanne mahaluki.

DUBA WANNAN: Makomar Lawal Daura bayan sabon nadi a DSS

An kama limamin dai da laifin shafe shekaru 10 yana bata yaran mutane birjik, inda batun ya sanya iyaye maza-maza su janye 'ya'yansu daga cocina domin gujewa 'aikin shaidan' a dakin Allah.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel