Shawarar da aka baiwa matasa masu bautar kasa gabanin zabukan 2019

Shawarar da aka baiwa matasa masu bautar kasa gabanin zabukan 2019

- Kuyi taka tsan tsan da yaudarar yan siyasa

- Kada ku yarda suyi amfani da ku wajen yin magudin zabe

- Wasu daga cikin ku zasuyi aikin zabe, dole ne ku nuna nagarta

Shawarar da aka baiwa matasa masu bautar kasa gabanin zabukan 2019

Shawarar da aka baiwa matasa masu bautar kasa gabanin zabukan 2019
Source: Facebook

Domin zaben 2019 dake gabatowa, shugaban CDs na NYSC, Yusuf Steve, ya gargadi yan bautar kasar da su gujewa yaudarar yan siyasa.

Yace yan bautar kasar su gujewa duk wani yunkurin yan siyasa don amfani dasu gurin yin magudin zabe.

Mista Steve yayi wannan jan kunnen ne a jawabin da yayi a sansanin yan bautar kasar dake Damare, kusa da Yola.

Yace yan bautar kasan zasuyi jami'an zabe a zaben 2019 dake gabatowa, don haka dole suyi abinda ya dace.

"Ku kasance masu nagarta domin gujewa bata wa NYSC suna" inji Mista Steve.

DUBA WANNAN: Yawan hayayyafa: Osinbajo ya koka

Ya jinjiinawa hukumar ta fannin tsaro da walwalar yan bautar kasar, amma ya horey su dasu kara dagewa ta fannin kula sakamakon cinyewar da ruwa yayi wa wasu yan bautar kasar na jihar Taraba a kwanakin baya.

Anyi wa yan bautar kasa 1,558 rijista a sansanin. 1,010 na jihar Adamawa, sai 548 na jihar Taraba.

Mista Mohammed, shugaban masu kula da sansanin, yace komai na tafiya daidai, akwai ruwa da wutar lantarki.

"Ina farincikin sanar da cewa yan bautar kasar nan sun nuna ladabinsu da dabi'u na gari wajen mu'amala da juna da kuma jami'an sansanin." inji Mohammed.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel