Ko meye makomar Lawal Daura, bayan da aka dawo da yaronsa DSS?

Ko meye makomar Lawal Daura, bayan da aka dawo da yaronsa DSS?

- Har yanzu Daura na hannun yan sanda ba tare da sun kai shi kotu ba

- An cafke shi ne bayan an sauke shi daga kujerar shi

- Wannan ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar

Ko meye makomar Lawal Daura, bayan da aka dawo da yaronsa DSS?

Ko meye makomar Lawal Daura, bayan da aka dawo da yaronsa DSS?
Source: UGC

Har yanzu tsohon shugaban DSS, Lawal Daura na hannun yan sanda ba tare da sun gurfanar dashi a gaban kuliya ba. Kwanaki 37 kenan tun da suka cafke shi bayan da Mukaddashin Shugaban kasa a lokacin, Yemi Osinbajo ya tsige shi daga kujerar shi.

Wani mai magana akan hakkin Dan Adam ya qalubalanci yanda aka aje Daura ba tare da kai shi kotu ba, domin hakan sabawa kundin tsarin mulkin kasar.

An kama Mista Daura ne a ranar 7 ga watan Augusta, jim kadan bayan Mista Osinbajo ya zarge shi da rashawa, amfani da kujerar shi don cimma wata manufa da kuma cin amana.

DUBA WANNAN: Ana so sojoji su daina sanya Unifom

An tsige shi ne bayan jami'an shi suka mamaye kofar shiga majalisa ba tare da wani dalili ba.

Da farko yan sandan sun aje shi ne a wani guri domin amsa tambayoyi. Amma majiyar mu ta gano an sake shi bayan kwana biyu, tare da tsananta tsaro akan shige da ficen shi. Washegari yan sanda suka maida shi ma'ajiyar su, inda suka ki kanshi kotu.

Wani babban jami'in tsaro yace Daura na ajiye a wani masaukin baki a Abuja amma ana barin shi ya ga iyalin shi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel